Daga - Mahadi Tukur Almizan
Joe Biden Ya Magantu: ZA MU YI DUK MAI YIWUWA WAJEN BAIWA TSARON ISRA'ILA KARIYA"
Shugaban ƙasar Amurka Joe Biden ya bayyana cewa ƙoƙarin Amurka na baiwa Isra'ila kariya bashida misali, ya siffanta hakan da 'ironclad', yayi wannan bayani ne a ranar Laraba yayin da ake cikin tsoron harin ɗaukar fansa daga Iran ko daga rundunonin ƴan gwagwarmaya sakamon harin da Isra'ila takai Ofishin jakadancin Iran dake Syria.
" Za mu yi duk abinda muke iyawa wajen baiwa tsaron Isra'ila kariya" cewar Biden, yayi wannan zantukan ne a lokacin da suke tare da Firaministan Japan Kishida Fumio a yayinda suke gabatar da taron manema labarai a Rose Garden.
Wannan kalamai sun biyo bayan maganar jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran da yayi lokacin huɗubar Eidin Ƙaramar Sallah inda ya jaddada cewa lallai zasu hukunta Isra'ila bisa harin 1 Afrilu wa da yayi sanadiyar Shahadar dakarun IRGC 7 ciki har da shugaban Quds Force na Syria da Lebanon.
Firaministan harkokin wajen Isra'ila Katz ya bayyana a wani saƙo da ya wallafa a X (Twitter) cewa "Idan Iran ta kawo mana hari daga Iyakokin ta, Isra'ila zata mayar da martani ta kaima Iran Hari".
Amurka da ta tabbatar da cewa Iran zata mayar da martani ba makawa kamar yadda Bloomberg suka tabbatar mata ta hanyar bayanan sirri.
Kwamandan CENTCOM Erik Kurilla ya garzaya Isra'ila a yau Alhamis, duk saboda razani da tsoron harin da kan iya zuwa daga Iran.
Duk a cikin razanin da aka shiga kamfanin jirgin sama na ƙasar Germany 'Lufthansa' ya dakatar da jigilar mutane daga Iran ko zuwa Iran, wannan dakatarwar ta fara aiki daga ranar 6 ga Afrilu.
0 Comments