Ministan Tsaron Isra'ila Ben Gvir Ya Yi Mummunan Hatsarin Mota : An Garzaya Da Mugu Asibiti.

 


A jiya Juma'a aka garzaya da ministan tsaron Isra'ila Ben Gvir zuwa asibitin dake kusa da birnin Ramla.

An garzaya da shi asibitin ne bayan ya yi mummunan hatsari inda motar shi ta hantsala ta juya a Central Israel.


Zaku iya ganin yadda motar ta hantsala a cikin bidiyon dake ƙasa, wanda aka wallafa a shafin X (Twitter)


Kafafen yada labaru na Isra'ila sun bayyana cewa ministan ya ketare jar danjar traffic 🚦 ne kafin faruwar hatsarin.

Ben Gvir yayi hatsari ne a lokacin da yake hanyar zuwa Ramla inda wata hatsaniya ta faru har aka caka ma wani wuƙa.

A halin yanzu jami'an ƴan sanda na bincike kan musabbabin hatsarin.

Domin samun Ingantacciyar Data cikin sauƙin da Rahusa a garzaya Playstore a sauke Application ɗin 👉 "Fadakdata"

Jaridar Times Of Israel ta kawo rahotanni da dama a watannin da suka gaba kan zargin motocin ministan da karya dokokin traffic 🚦.

Kafafen yada labarun Isra'ila sun bayyana cewa halin ministan ne saba dokokin traffic ɗin, domin a kodayaushe yana baiwa direba umarnin ƙin bin dokar traffic 🚦



Ko a watan August na shekarar da ta gabata sai da ministan yayi hatsari sakamakon ketare jar danjar traffic 🚦 yayin da ke hanyar zuwa Interview.

Post a Comment

0 Comments