Daga - Mahadi Tukur Almizan
Dubunnan Isra'ilawa ne suka fito gagarumar Zanga Zanga a Jiya asabar suna masu neman ayi sabon Zaɓe sannan kuma gwamnati ta ɗauki matakan dawo masu da ƴan uwan su dake tsare a Gaza, wannan dai zanga zanga ce ta adawa da Benjemin Netanyahu.
Zabga zangar dai na cigaba da gudana lokaci bayan lokaci tsawon watannin da aka yi ana yaƙi tsakanin Isra'ila da Hamas wanda ake cikin wata na bakwai, Isra'ilawan dai na cikin fushin cigaba da kasancewar ƴan uwan su 133 a hannun Hamas, kuma suna ɗora laifin hakan akan Netanyahu ne.
Domin samun data mai inganci cikin sassauƙan farashi Ku sauke Application ɗin Fadakdata anan 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.absoft.fadakdata
Wani bincike ya nuna cewa kaso mafi yawa na al'ummar Isra'ila suna ɗora ma Netanyahu alhakin faruwar harin 7 October da Hamas ta kai Isra'ila, a cewar su wannan gazawar tsaro daga gwamnatin ta Netanyahu.
Netanyahu dai shine Firaministan Isra'ila mafi daɗewa akan kujera ya bayyana cewa yin sabon zaɓe a halin da ake ciki zai amfani Hamas ne kawai.
A Lokacin wata zabga zanga da ta gudana a watan March da ya gabata wani daga cikin masu zanga zangar mai suna Yalon Pikman mai kimanin shekaru 58 ya bayyana cewa " Mun fito wannan zanga zangar ne muna masu adawa da gwamnati a bisa cigaba da durƙusar damu da take tsawon watanni bakwai muna cigaba da durƙushewa", kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa.
Domin samun data mai inganci cikin sassauƙan farashi Ku sauke Application ɗin Fadakdata anan 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.absoft.fadakdata
Kafafen yada labarai na Isra'ila sun bayyana cewa dakarun Hamas sun kama mutane 253 sannan kuma sun kashe aƙalla mutum 1,200, an saki wasu daga cikin kamammun ta hanyar musayar fursuna a watan November na shekarar da ta gabata wasu kuma suna tsare hanyar yanzu, wannan na daga cikin abinda ya harzuƙa al'ummar Isra'ila kuma ya sa suke adawa da Netanyahu.
" Mama ta mai suna Yocheved Lifshitz mai shekaru 85 tana daga cikin wadanda aka saki daga kamammun, sai dai Mahaifin mu yana can tsare hannun Hamas haryanzu" cewar Sharone Lifschitz mai shekaru 52 a duniya.
0 Comments