Daga - Yusuf Kabir
Amurka da abokananta suna son jefa Iran cikin Yakin Dufanil Aqsa ta yadda za ta rika kaiwa Isra'ila hare-hare kai tsaye a zahiri;babbar manufarsu durkusar da Iran ta fuskacin tattalin arziki da shagaltar da ita daga bunkasar da take yi a bangarori mabambanta.Ga wasu nazarce-nazarce a kan lamarin:-
1.Amurka ce kai tsaye ke kashe Palasdinawa a Gazza tsawon watanni 6,badan taimakon Amurka ba,da yanzu Isra'ila ta rushe"Sayyid Nasrallahi ya bayyana haka
2.Tabbas Iran ba ta jin tsoron yaqi,domin 'Ya'yan Imamu Husaini (as) ne su,kowa ya san jarumatar gidan annabta (as) suna da fikirar Imamu Ali (as) ta rashin jin tsoron mutuwa a sad da yake cewa:"Wallahi dan Abu Dalib ya fi jin dadi da shaukin mutuwa, fiye da yadda yaro ke shankin nonan Mahaifiyarsa."
3.Matukar Isra'ila ko Amurka suka kai hari kai tsaye cikin Iran,to labudda za su kai hari kai tsaye cikin Isra'ila.
4.Iran ba ta gaggawar daukar matakin barnar da aka yi mata cikin gaggawa,ba ta zumudi,rawar jiki,gaggauwa,ba ta aiki da fushi kamar yadda maqiyanta ke yi,tana bin dokokin 'yan adamtaka da dokokin yaqi na duniya hakan ya sa ba ta yaqar mata ko yara.Mu kalli hatta baya shahadar Gen.Qaseem Sulaimani ba ta kai hari a kan yara ko mata ba,a'a ta kai hari ne a kan Sansanin Sojan Amurka da ke Iraki da ake kira "Ainul-Asad" Sannan daga baya sun halaka shugaban CIA din da ya jagoranci kashe Sulaimani din ta hanyar kai hari kan jirgin da yake ciki.
KAIFIN BASIRAR IRANIYAWA A SIKELI
Allah ya horewa mutanrn kasar Iran basirar kwakwalwar da ta zarce ta Larabawa da Yahudawa,hakan ya sa su lalubo hanyoyin ci gaban kasar su bayan Saddam Husaini ya afka mata da yaki bisa umarnin iyayen gidansa.A lokacin yakin an sami shahidai kimanin Miliyan biyu,a jawabin da Imam Khumaini (ks) ya yi ya karfafi samun dakarun sa kai,a lokacin dakarun IRGC ba a jima da kafa su ba,amma mu kalli ci gaban da ta yi cikin shekaru 40+ da juyin,wannan yana nu na girman basirarsu da kuma imaninsu da abunda suka sanya a gaba.Fitaccen mai sharhi a kan siyasar gabas ta tsakiya Comrade Adamu Abu Baqra yana cewa:"Tunanin qasar Farisa ya wuce sanin irin al'ummar da suke zagaye da su kamar Larabawa da Turkawa da kuma Qurdawa maqotan su, tunaninsu a game da Duniya irin tunanin Yahudawa ne da suka dora manyan daulolin duniya a matsayin da suke a halin yanzu, shi yasa take challenging manyan qasashe da suka zama allolin qasashen larabawa don su nuna musu cewa dukkan abinda ake nuna musu qaryar banza ce, idan za su dawo cikin haiyacin su su dawo.
Idan da zaka ka lura da kyau zaka samu cewa Bayahuden mutun musamman irin na Izra'el baya shigo da kowa cikin tunanin sa saboda tsaro, sannan shi ake nema ayi hadin gwiwa da shi don samar da wata fasahar, haka zalika Bafarisen qasar Iran shi ma yake baya shigo da kowa cikin tunanin su saboda tsaro."
IRAN DA HANA AMURKA DA KAWAYENTA RAWAR GABAN HANTSI A GABAS TA TSAKIYA
Jaridar Daily beast,May 18,2019 ta wallafa muqalar fitaccen dan Jaridar nan Ba'amurke da ake kira Michael Weiss a kan tasirin Iran a gabas tsakiya da yadda ta cika kasashe da Dakarun da suke karbar umarni kai tsaye daga gare ta yana cewa:"Karfin Iran ta hannun Sulaimani ya fadada tare da gawurta ta yadda Iran ta sami damar kafa rundunonin da ke iko da gabas ta tsakiya daga Tehran har ya zuwa farin kogi na tsakiya."
Weiss ya ci gaba da cewa:"Sulaimani a karkashinsa akwai dakaru sama da 100k wadanda galibansu ba 'yan Iran ba ne ba,wasu ma ba larabawa ba ne,akwai 'Yan Pakistan,Afganistan.
Michael Weiss yana ganin Sulaimani ya fi shuwagannin Amurka uku da suka hada da Obama,Donal Trump na yanzu kaifin basira.
Manazarci Adamu Abu baqra yana cewa:"A gefe mu kace qasar Iran kusan duk in da America take da base sai ita kuma ta samar da wadanda za su yi mata qafar Ungulu a wajen.
Kusan duk qasashen Larabawa da suke gabas ta tsakiya da yardar su qasar Amurka ta yi sansani a cikin qasashen su in banda qasashe guda biyu da tayi amfani da qarfi ta bude su qasashen sune Iraq da Syria.
Ta bude na Iraq lokacin da tayi yaqi da Saddam, sannan ta bude na Syria domin yaqar yan ISIS da kuma bawa alummar qasar kariya daga kisan kiyashin da suka ce wai shugaba Asad yana yi musu.
Bayan qasar Iran da Amurka daga cikin qasashen da suke cikin gwagwarmayar mallakar gabas ta tsakiya Akwai qasar sSaudiya da kuma Turkey, kuma kowacce da irin salon da take bi wajen mamayar yankin; sannan suna hada rundunoni domin bacin rana.
Duk wata qungiya da ka ji ta a gabas ta tsakiya tana amsa sunan muqawama ko "resistance" to kar ma ka bata lokaci wajen neman wacece uwar gidan ta Iran ce, idan kuma ka ji an ambaci jihad a qarshen sunan qungiya to ko dai Saudiyya ko kuma turkey tare da hadin gwiwa da wasu qasashen da suke bin mazhabin Sunnah in ka dauke qungiyoyi biyu wadanda na sunnah ne qasar iran tayi "hijacking" din su daga wajen iyayen gidan su kamar HARAKAT AL MUQAWAMA AL ISLAMIYYA (HAMAS) da kuma ISLAMIC JIHAD dukkan su a Gaza mallakin sunnah ne a da.
Qasar Saudi fitattaun qungiyoyin ta sune AL QA'IDA IN THE ARABIAN PENINSULA A. Q. A. P da, AL'QA'IDA CENTRAL sai babbar rundunarta lashkar taiba dake pakistan, da wasu qanana a cikin qasar Iraq da Syria.
Amma kuwa ita Iran ta mamaye qasashen gabas ta tsakiya da tulin mayaqa wadanda suke karbar umarni guda daya sabanin mayaqan jihadin sunnah wadanda sukan karbi umarni ne kawai daga qasar da take temakon su.
A cikin qasar Iraq kawai Iran tana da qungiyoyi irin su
Kata'ib Hizbullah,
Asab-Ahlil haqq,wacce a yanzu suke cewa national resistance movement,
SYRIA
harakat hizbullah al Nujaba,
Kata'ib saiyidush shuhada
Badr organization,
LEBANON
hizbullah the sophisticated,
A YEMEN
Ansarullah, a
PAKISTAN
zainabiyyun a
AFGHANISTAN
Fatimiyyun
BAHRAIN
saraya al ashtar, ba'a yi mata umarni ba,
Saraya al mukhtar ita ma haka.
Ana zargin tana da runduna a cikin Saudiyya
Wato Hizbullah Alhijaz
Wadannan rundunonin gaba daya umarni daya suke dauka shine shugaban juyin juyahalin musulunci na Iran."
A takaice dai dama Iran ce ke bayan Hizhullahi har ta yi nasara a yaqinta da Isra'ila a 2006,sannan ita ke bayan Asad har ya yi nasara daga kawar da shi da shi daga kan mulki na tsawon shekaru, sannan ita ce ke bayan dakarun Iraki har suka yi nasara a kan 'yan ta'addan Isis daga mamaye Iraki,ita ke bayan Jaishil Mahdi har suka kori NATO da tilasta musu ficewa daga Iraki a 2003,ita ke bayan Putin na Rasha har yanzu ba a yi nasara a kan sa ba;ita ke bayan Yemen har suka sami nasara a kan Saudiyya da kawayenta,ita ke bayan canza akalar siyasar 'Yan Taliban tare da mayar da su masu jin kai da tausayi bayan sun kasance masu zafin rai.
A takaice dai tabbas Iran za ta dauki mataki bisa kashe Mata Birgediya Janar Muhammad Reza Zahedi da Mutane 6 da Isra'ila ta yi a Ofishin jakadancin Iran da ke Siriya;amma yaushe za ta kai harin,wace siga za ta kai, to wannan lokaci ne zai nuna.
Kabir Yusuf:Dan Jarida ne Marubuci mai sharhi a kan siyasar gabas ta tsakiya.
Fri:12/14/2024.
11:45am.
Za a iya samunsa a :kabiruyusuf533@gmail.com.09063281016.
0 Comments