Ƴan sandan Faransa sun yi nasarar kama wani mutum da yayi yunkurin tarwatsa kanshi da Bom a ofishin jakadancin Iran da ke babban Paris birnin ƙasar Faransa.
Majiyar jami'an ƴan sandan Faransa ta bayyana ma kafar yaɗa labarai ta Reuters cewa anga mutumin da misalin karfe 11 na safe agogon GMT, yana ƙoƙarin shiga Ofishin jakadancin yana ɗauke da wani abu kamar Gurnet (Grenade) da rigar bom.
Daga baya mutumin yabar ofishin jakadancin sannan jami'an ƴan sandan suka cafke shi, yana ɗauke da "Replica Grenades".
Majiyar ta ƴan sandan ta tabbatar da cewa wannan mutumin dai shine aka zarga da kokarin cinna ma ofishin jakadancin wuta a watan September na shekarar da ta gabata.
Mutane da yawa sun tabbatar da mutumin ya ja tuta a kasa yana me faɗin cewa yazo daukar fansar jinin ɗan uwan shi kamar yadda jaridar "Le Parisien" ta wallafa a shafin ta.
Domin samun Data mai inganci da rahusa Ku sauke Application ɗin Fadakdata anan 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.absoft.fadakdata
Sai dai ba a tabbatar da inda ɗan uwan nashi da yake iƙirari ya mutu ba, ko yana da alaka da rikicin dake tsakanin Iran da Isra'ila ko ba ya da alaka.
Ofishin Jakadancin Amurka dake birnin na Paris ya umarci Amurkawan da ke aiki a wajen su kaurace ma unguwar, kamar yadda ƴan sandan Faransa suka bukata.
©️ Freedom Fighters Ng
0 Comments