Yadda Aka Kashe Ƴaƴan Shugaban Sashen Siyasa Na Hamas Isma'il Haniyeh Guda Uku.

 


Ƴaƴa uku da jikoki biyu sunyi Shahada, jikarshi ɗaya ce kawai ta tsira daga motar .

Daga - Mahadi Tukur Almizan

Isma'il Haniyeh ya tabbatar da Shahadar ƴaƴan shi uku a wani harin jirgin sama da Isra'ila ta kai Gaza wanda  daga baya Isra'ila ta tabbatar da cewa sun nufi waɗannan ƴaƴan nashi uku ne dama.


Lamarin ya faru ne a shekaran Jiya Laraba, kafar yaɗa labarai ta Aljazeera ta labarto cewa  ƴaƴan Haniyeh uku ne suka yi shahada tare da jikokin shi dale cikin motar da Isra'ila ta hara a Shati Camp dake arewacin Gaza.



Cikin bidiyo zaku ga yadda harin yayi kafa kaca da motar ansamu ragowar jikin mutum ɗaya👇


Haniyeh dai yana zaune ne yanzu a Doha babban birnin ƙasar Qatar daga can ne ya tabbatar wa manema labarai ingancin labarin ta hannun wata kafar yaɗa labarai dake me alaƙa da Hamas 'Shehab News Agency'.



"Dukkanin al'ummar gaza  sun sadaukar da jinanen ƴaƴan su da dangin su, nima ɗaya ne daga cikin su" cewar Isma'il Haniyeh


Shehab News Agency ta bayyana ƴaƴan nashi a matsayin Hazem, Amir da Mohammad Haniyeh da kuma jikokin shi ɗiyar Hazem mai suna Amal da ɗan Amir mai suna Khalid da ƴar Khalid ɗin mai suna Rezan duka sunyi shahada a harin.



Isma'il Haniyeh dai yana da ƴaƴa 13 ne baki ɗaya.


A watan da ya gabata wata jaridar Isra'ila ta labarto cewa ƴan sandan Isra'ila sun kama ƴar uwar Haniyeh a kudancin Gaza, ƴar uwar tashi tana zaune ne a Isra'ila an zarge ta da alaƙa da Hamas kamar yadda kafar yaɗa labaran ta labarto.


A ranar Laraba shugaban ƙasar Turkiyya Tayyip Erdogan da Firaministan Turkiyya Hakan Fidan sun miƙa saƙon ta'aziyya ga Haniyeh ta wayar tarihi.


Mai magana da yawun sojin Isra'ila Daniel Hagari ya tabbatar da faruwar harin a ranar Laraba, a wani saƙo da ya wallafa a shafin X (Twitter) Hagari ya bayyana cewa sojin Isra'ila sun hari ƴaƴan Haniyeh guda uku, a cewar sa wasu suna hanyar zuwa aikata ta'addanci a tsakiyar birnin Gaza, Hagari ya bayyana cewa ƴaƴan na Haniyeh duk sojoji ne.

Post a Comment

0 Comments