Zanga Zangar Da Ta Ɓarke A Jami'o'in Amurka, An Kama Sama Da Mutum 120.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Zanga zangar nuna goyon bayan Palasɗinawa gami da nuna adawa da ta'addancin Isra'ila a Gaza ta ɓarke a jami'o'in ƙasar Amurka aƙalla 24.


Sama da mutum 120 ne jami'an ƴan sanda suka kama a jami'o'in mabanbanta a ranar 24 ga watan Afrilun da muke ciki a kokarin da jami'an tsaron suke yi na tarwatsa zanga zangar.



Masu zanga zangar dai suna neman Amurka ta gaggauta dakatar da duk wani taimako da take yi ma Isra'ila a ta'addancin da take yi a Gaza.


Jami'an tsaro ɗauke da muggan makamai aka jibge a Jami'ar Columbia, jami'ar New York, da jami'ar Austin dake Texas da jami'ar Southern California domin daƙile zanga zangar.



Wasu na ganin hakan a matsayin take haƙƙin faɗar albarkacin baki daga mahukuntan gwamnatin Amurka dake ƙaryar kare ƴancin ɗan Adam.



A bisa zargin ƙin jinin Yahudawa ko barazana da yaƙar Yahudawa hukumomin Amurka suna ta kokarin dakile yunkurin ɗalibai na nuna goyon bayan Palasɗinawa.


Gwamnan jihar Texas a wani rubutu da ya wallafa a kafar sada zumunta ya bayyana cewa " Duk ɗaliban da aka samu sun yi musharaka a zanga zangar to za a kore shi daga makaranta".


Wani Farfesa Bayahude mai suna Jeremi Suri ya bayyana wa kafar yaɗa labarai ta Aljazeera cewa "Ɗaliban suna rera taken 'Free Palestine' ne kawai, suna cikin rera wannan take sai naga ƴan sandan ƙasa da ƴan sandan makaranta da Army Police sun shiga cikin Ɗaliban suna kama su".



Sai dai duk da wannan kamen da barazanar da hukumomin suke yi zanga zangar tana kara bazuwa a faɗin Amurka.


Shima Netanyahu yayi magana dangane da wannan zanga zanga da ta ɓarke a Amurka ya ce "Lallai ayi wani abu domin dakatar da wannan zanga-zangogin na goyon bayan Palasɗinawa a Amurka".



Post a Comment

0 Comments