An Hana Likitan Da Zai Bada Shaidar Kisan Kiyashin Da Isra'ila Ta Yi A Gaza Shiga Turai.

 


Daga- Mahadi Tukur Almizan

Gwamnatin kasar Germany ta sanya ma Dr. Ghassan Abu Sitta takunkumin shiga Turai , wanda aka shirya zai bada shaidar ganin ido na ta'addancin Isra'ila a Gaza a gaban majalisar kasar Faransa.


An hana Dr. Ghassan shiga Faransa ne a ranar asabar 4 ga watan Mayu, yayin da yake hanyar zuwa yayi magana a majalisar dattawan kasar Faransa kan ta'addancin Isra'ila a Gaza.


A tashar jirgin sama ta 'Charles De Gaulle' hukumomin Faransa suka sanar da shi cewa kasar Germany ta saka mashi takunkumin shiga kasashen Turai.



A wani saƙo da ya wallafa a shafin sa na X, Dr. Ghassan ya bayyana cewa " Ina tashar jirgin sama ta Charles De Gaulle an hana ni shiga Faransa, inda zan je until magana a majalisar dattawan ƙasar a yau, sun ce Germany ta sanya  man takunkumin shiga Turai har na tsawon shekar 1".


Dr. Ghassan ya bayyana cewa wannan yunkuri ne na rufe bakin shaida akan ta'addancin Isra'ila kamar yadda suka kashe Dr. Adnan al-Bursh likita ne da suka azabtar dashi har ya mutu a kurkukun Isra'ila a watan da ya gabata.


Dr. Ghassan Abu Sitta likita ne dan kasar England kuma shine Director na Conflict Medicine Program a American University dake birnin Beirut na ƙasar Lebanon, yana Gaza a satittukan farko na wannan yaƙin, a watan Nuwamba da ya dawo England ya bada shaida a wani kwamitin laifukan yaki hakanan ya bada shaida ga wasu masu bincike daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC).


©️ Freedom Fighters Ng

Post a Comment

0 Comments