Ansarullah Na Yemen Sun Bude Sabuwar Fuskar Yakar Isra'ila : Za Su Fara Harar Jiragen Isra'ila A Bahar - Rum (Mediterranean Sea)

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Yemanawa sun dauki aniyar faɗaɗa Operations ɗin su na yakar Isra'ila zuwa tekun Bahar-Rum wanda da turanci ake kira 'Mediterranean Sea'.


A ranar 3 ga watan Mayu da muke ciki rundunar sojin Yemen ta fitar da sanarwar cewa an shiga fuska ta huɗu a yaƙin su da Isra'ila a cigaba da goyon bayan al'ummar Palestine, sojin na Yemen sun yi barazanar harar duk wani jirgi mai alaƙa da Isra'ila a duk inda hare haren su za su iya kaiwa.


Hare haren sojin na Yemen sun yi nasarar hana Isra'ila sufuri a tekun Red Sea, a yanzu kuma za su faɗaɗa wannan yaƙi zuwa Mediterranean Sea.

A farkon shekarar nan ne sojin na Yemen suka faɗaɗa hare haren na su zuwa Indian Ocean, Wanda hare hare a wannan teku ya shafi tattalin arzikin Isra'ila sosai.

A ranar juma'a Gwamnatin Yemen ta gargadi Isra'ila kan shirin afkawa Rafah dake kudancin Gaza.

Sanarwar faɗaɗa yakin ta fito ne daga mai magana da yawun sojin na Yemen Birgediya Janar Yahya Saree, yayi wannan sanarwa ne a gaban dubunnan al'ummar Yemen da suke taruwa a babban birnin ƙasar a juma'ar kowane sati domin nuna goyon baya ga al'ummar Gaza.


Tun tsakiyar watan Nuwamban shekarar 2023 dakarun na Yemen wuka tare duk wata hanyar wucewar jiragen dakon Isra'ila da masu alaƙa da su a Red Sea, duk da cewa Amurka da ƙawayen ta sun yi ta kai hare hare kasar amma Yemanawa sunyi nasara a wannan aiki.

Za a iya cewa Amurka ta faɗi a yakin ta da Yemenawan har sai da ta kai ga Amurka ta yi ma Yemen tayin cewa zata gyara duk wata ɓarna da tayi a Yemen kuma zata kwashe duk wasu dakarun kasashen waje dake fadin ƙasar har ma waɗanda suke a tsibiri sannan kuma za su cire sunan Ansarallah daga jerin sunayen ƙungiyoyin ƴan ta'adda da sharaɗin cewa za su dakatar da hare haren su akan jiragen Isra'ila su zama ƴan baruwana a cikin wannan yaƙin - kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida ma kafar yaɗa labarai ta The Cradle.



Post a Comment

0 Comments