BINCIKE: Da Makamin Amurka "JDAM" Isra'ila Ta Yi Amfani Wajen Kaima Jami'an Lafiya Hari A Lebanon.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Kafar yaɗa labarai ta 'The Guardian' ta wallafa wani rahoto da ya bayyana cewa Isra'ila ta yi amfani da makamin Amurka wajen kaima jami'an lafiya hari a kasar Lebanon wanda yayi sanadiyyar mutuwar ma'aikatan lafiyar 7 a kudancin Lebanon.


Rahoton na The Guardian ya bayyana cewa an samu baraguzan kwanson bom din da aka kai harin da shi a inda lamarin ya faru, kuma hukumar kare hakkin dan Adam ta duniya "Human Rights Watch" ta bayyana cewa wannan harin ya saɓa ma dokokin ƙasa da ƙasa na majalisar dinkin duniya.


Ma'aikatan lafiyar dake aikin sakai da sukayi shahada a wannan harin suna da shekaru tsakanin 18 zuwa 25 a ranar 27 ga watan March da ya gabata.


Lamarin ya faru ne a Ambulance Center 🚑 na ƙungiyar "Lebanese Succor Association" a garin al-Habariyeh dake kudancin Lebanon a ranar ta 27 ga watan March.



Waɗanda suka fara zuwa wurin da lamarin ya faru sun samun baraguzan bom din da aka kawo harin ƙirar Amurka da ake kira "Joint Direction Attack Munition" (JDAM), hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta "Human Rights Watch" da wasu ƙwararru n masana tsaro ne suka gudanar da bincike kan baraguzan suka tabbatar da baraguzan "JDAM" ne ƙirar Amurka.


Wannan makami na "JDAM" dai Isra'ila ta yi amfani dashi a Gaza da Lebanon a hare mabanbanta kuma yana daga cikin makaman da tafi karba daga hannun Amurka.

Bayan kwanaki biyar da wannan harin ne dai Isra'ila ta sake kai hari kan masu bada agajin gaggawa dake aiki karkashin "World Central Kitchen" a Gaza, wannan harin dai ya jawo ma Isra'ila ƙarin bakin jini musamman a ƙasashen Yamma, sai dai Isra'ila ta bayyana wannan harin a matsayin babban kuskure da ta aikata.

Post a Comment

0 Comments