Daga - Mahadi Tukur Almizan
A karo na 6 zaratan dakarun sojin Ansarullah na Yemen sun kakkaɓo leƙen asirin Amurka da ake kira 'US MQ-9' a yau Laraba 29 May 2023.
Sanarwar kakkaɓo wannan jirgi ta zo a rana daya da rundunar ta kai ma wasu jiragen ruwa 6 hari a tekuna mabanbanta.
Jirgin na US MQ-9 ya bayyana a sararin samaniyar Yemen a yau 29 May sai dai dakarun na Houthi sun yi nasarar sauke shi ƙasa kamar yadda zaku gani a bidiyon da ke ƙasa.
BREAKING | The downing of yet another US MQ-9 drone by the Yemeni Armed Forces in Marib. pic.twitter.com/oNGQlzr3OS
— The Cradle (@TheCradleMedia) May 29, 2024
Kamar yadda kukaji dai wannan shine karo na shida da Yemenawan suka harbo kalar wannan jirgin na Amurka, na baya bayan nan karo na 4 ya faru ne a ranar 17 ga wannan watan, karo na 5 kuka ya faru ne a ranar 21 ga wannan wata na Mayu.
Ƙimar darajar wannan jirgi ta kai kimanin dalar Amurka miliyan 30 ($30 Million).
Tun farkon wannan shekarar ne dai Amurka da Ingila suka kulla alaƙar kaima Yemen hare hare saboda hare haren da dakarun na Ansarullah suka kaddamar kan duk wani jirgi mai alaƙa da Amurka a watan November na shekarar da ta gabata domin nuna goyon baya ga Palasɗinawa da kuma tursasa Isra'ila domin ta dakatar da hare hare kan al'ummar Palestinu.
Sai dai wannan ƙawancen na Amurka da Ingila bai yi nasarar dakatar da hare haren Yemenawa ba sai dai asara da kunyata da take jawo masu a kullum.
Su kuma Yemenawa a gefe guda kara faɗaɗa hare haren su suke yi, a halin yanzu suna kai hare hare a Red Sea, Indian Ocean yanzu ma har Mediterranean Sea Kai sun ma fadi cewa zasu hari jiragen Isra'ila da masu alaƙa da su a duk inda makaman su suke iya kaiwa.
A yau din dai dakarun na Ansarullah sun bada sanarwar cewa sun hari jirage 6 a tekuna mabanbanta ta hanyar amfani da Missiles da Drones, sun hari jirage guda uku a Red Sea sai kuma wasu jiragen jiragen yaƙin Amurka 2 a Arab Sea, sai kuma wata Tankar mai a tekun Mediterranean Sea.
BREAKING | Yemeni Armed Forces announce the targeting of 6 ships in 3 seas with missiles and drones:
— The Cradle (@TheCradleMedia) May 29, 2024
Red Sea:
- Bulk carrier LAAX was targeted, hit, and significantly damaged.
- Bulk carrier MOREA was targeted.
- Bulk carrier Sealady was targeted.
Arabian Sea:
- US bulk… pic.twitter.com/D6iSKTmd04
A farkon watan May da muke ciki ne dakarun na Yemen suka bayyana cewa za su faɗaɗa hare haren su har Mediterranean Sea wato Bahar-Rum.
Hakanan dakarun na Ansarullah a kullum suna kara jaddada cewa ba za su dakatar da wadannan hare haren ba har sai Isra'ila ta dakatar da kashe Palasɗinawa.
0 Comments