Iran Ta Saki Ma'aikatan Jirgin Isra'ila Da Ta Kama, Ta Ci-gaba Da Riƙe Jirgin.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

A watan da ya gabata ne jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cafke jirgin dakon kaya na Isra'ila bisa karya dokokin sufuri a teku, ƴan sa'o'i kaɗan kafin ta kai harin ramuwa kan Isra'ila a watan Afrilu inda ta harba ɗaruruwan missiles zuwa Isra'ila.


A ranar 2 ga watan Mayu da mu ke ciki ne wasu jami'an gwamnatin Iran 2 suka bada sanarwar sakin ma'aikatan jirgin (Crew)  mai alaƙa da Isra'ila wanda dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) suka kama a mashigar Hormuz.


Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir Abdollahian ya bayyana sakin ma'aikatan jirgin karamci ne na ƴan adamtaka domin ma'aikatan su koma gida ciki har da ƴan kasar Estonia, ya bayyana haka ne a lokacin da suke sanya ta wayar tarho da takwaranshi na Estonia Margus Tsahkna.


Kafar yaɗa labarai ta Tasnim ta labarto ƙarin wasu zantuka na Ministan inda yake cewa "Jirgin kuma yana tsare ne bisa kulawar hukumomin Shari'a bisa laifin da ya shafi harkar tsaron teku sakamakon kashe Radar jirgin da suka yi a lokacin da suka shigo yankin iyakar ƙasar Iran a tekun".


A nashi bangaren ministan harkokin wajen ma Estonia ya mika godiya ga jamhuriyar Musulunci bisa wannan karamci na ƴan adamtaka da tayi na sakin ma'aikatan kamammen jirgin.


Hakanan kuma ministocin kasashen biyu sun tattauna akan yadda za su kara kyautata alaƙar kasashen biyu, wato Estonia da Iran kuma sun tattauna akan halin da al'ummar Gaza ke ciki da bukatuwar haɗin kai domin kawo karshen yaƙin.


A ranar 13 ga watan Afrilun da ya gabata ne IRGC suka kama jirgin na Isra'ila 'MSC Aries Container Ship".

Post a Comment

0 Comments