Daga - Mahadi Tukur Almizan
A kalla sojojin Syria 8 ne suka jikkata sakamakon harin da Isra'ila ta kai kusa da babban birnin ƙasar ta Syria Damascus.
Harin da jikkata sojojin na Syria ya faru ne a yammacin ranar 2 ga watan Mayu da mu ke ciki.
"Da misalin ƙarfe 10:05 na ranar Alhamis haramtacciyar kasar Isra'ila ta kawo ma Syria hari daga ɓangaren Golan na kasar Syria, sun hari wani muhalli kusa da birnin Damascus, wannan hari yayi sanadiyyar rauna ta jami'an tsaron Syria guda 8 da kuma asarar wasu kayayyakin soji" kamar yadda majiyar jami'an tsaron kasar ta sanar da kafar yaɗa labarai ta ƙasar SANA News Agency.
Ku garzaya Fadaktelcomms domin samun data mai inganci da rahusa
Hakanan kafar yaɗa labarai ta Reuters ta bayyana cewa wata majiya da bata bayyana ma ta sanar da su cewa Isra'ila ta hari wani muhallin jami'an tsaron Syria a ranar Alhamis da dare.
Wakilin kafar yaɗa labarai ta Sputnik's da ke Syria ya labarto cewa jami'an sojin na Syria sun yi kokarin kakkaɓe makaman na Isra'ila da Aird Defense ɗin su.
Tsawon shekaru kenan dai Isra'ila na kaima Syria hari a cewar Isra'ila hukumomin ƙasar ta Syria yan koren Iran ne da Hezbollah suke baiwa Iran damar taimaka ƴan gwagwarmaya a Lebanon.
0 Comments