Masu Zanga-Zangar Goyon Bayan Palasɗinawa A Mexico Sun Cinna Ma Ofishin Jakadancin Isra'ila Wuta.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

A daidai lokacin da ake cigaba da zanga zangogin nuna goyon bayan al'ummar Palestinu a faɗin duniya kasashen Yamma sun nuna cewa basu da wani dalilin yanke alaƙar soji da Isra'ila, wato ba za su yanke tallafawa ma Isra'ila da soji da makamai ba.

Wannan ya ƙara tunzura al'ummar kasashen Yamma hakan kuwa ya haifar da gagarumar zanga zangar adawa da Isra'ila gami da nuna goyon baya ga al'ummar Palestinu a birnin Mexico a ranar Talata 28 May.

Zanga zangar ta gudana ne a bakin Ofishin jakadancin Isra'ila, sai dai masu zanga zangar sun yi arangama da jami'an ƴan sanda a bakin Ofishin jakadancin.

Arangamar tsakanin masu zanga zangar da ƴan sanda ta ɓarke me yayinda masu zanga zangar suka yi kokarin kawar da shingen da zai hana su isa Ofishin jakadancin na Isra'ila, rikici ya barke inda ƴan sandan suka rika harba barkonon tsohuwa su kuma masu zanga zangar suka jifa da duwatsu da kuma  jefa wuta ta hanyar amfani da kwalaben Molotov Cocktail.


 


Sakamakon wannan arangama an tabbatar da jami'an ƴan sanda aƙalla 6 suka samu raunuka, masu zanga zangar kuma sun yi nasarar cinna ma gaban Ofishin jakadancin na Isra'ila wuta.


Wannan zanga zangar dai ta biyo bayan awa ɗaya ne da gwamnatin Mexico ta sanar da buɗe file na shelanta shiga cikin Case ɗin da South ta kai karar Isra'ila Kotun Duniya (ICJ).


Gwamnatin ta shelanta kudurinta na shiga case a cewar ta zata bayyana matsayar ta da bayanai masu alaka da case ɗin, hakanan gwamnatin zata  tattauna akan hana kayan agaji da Isra'ila tayi su isa Gaza da kuma rusa abubuwan tarihi na al'ummar Palestinu.


Duk da wannan matsayar da gwamnatin ta Mexico ta ɗauki ana ganin shugaban kasar ta Mexico Andres Lopez Obrador yana a tsaka tsakiya dangane da al'amarin ta'addancin Isra'ila a Gaza.

Ana ta kara samun ɓarkewar zanga zangogin adawa da Isra'ila musamman sakamakon ƙaruwar ta'addancin su kan Palestinu ciki har da kisan kare dangin da suke yi a Rafah, wannan yasa dubunnan al'ummar kasashen Yamma suka fito a birane mabanbanta suna kiran gwamnatocin su su yanke alaka da Isra'ila.

Sai dai a gefe guda duk da girmamar wannan ta'addancin na Isra'ila a Rafah Amurka ta bayyana a fili cewa wannan  kisan Isra'ila tayi a Rafah bai isa ya zama wani jan layi da zai sa ta yanke gudummawar makamai da take baiwa Isra'ila ba.


Post a Comment

0 Comments