Daga - Mahadi Tukur Almizan
Rahotanni na nuni da cewa Firaministan Isra'ila Benjemin Netanyahu ya shiga damuwa sosai bisa yiwuwar cewa ICC zata bada umarnin kama shi.
Kafafen yada labaran Isra'ila sun bayyana cewa Amurka na kokarin baiwa Netanyahu kariya daga kamun kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) bisa zargin aikata kisan ƙare dangi a Gaza.
Shafin labarai na Walla ya labarto cewa Netanyahu yana ta matsa ma fadar Gwamnatin Amurka 'White House' ta hanyar kiran waya akan lallai su bashi kariya daga kamun ICC.
Hakanan jaridar Isra'ila mai suna "Maariv" ta wallafa wani rahoto da ya bayyana cewa Netanyahu ya shiga babbar damuwa a yanzu bashi da natsuwa saboda tsoron yiwuwar kamun ICC.
Ko kasan cewa zaka iya samun data cikin sassauƙan farashi a FadakTelcomms ku garzaya Playstore ku sauke Application ɗin mu 👉 https://play.google.com/store/apps/details?id=co.median.android.xaqakw
Wata mjiya mai kusanci da jaridar ta bayyana bada umarnin kama Netanyahu magana ce ta lokaci kawai amma babu makawa sai ICC ta bada umarnin kama shi.
Hakanan jaridar ta bayyana cewa akwai yiwuwar a haɗa har da ministan tsaron Isra'ila Yoav Galant da Major General Herzi Halevi duka a kama tare da Netanyahu.
A ranar 26 ga watan April da ya ƙare Netanyahu ya wallafa wani sako a kafar sada zumunta ta X (Twitter) inda ya bayyana cewa " A ƙarƙashin mulki na Isra'ila ba zata lamunci duk wani yunƙuri daga Headquarter ICC dake Hague ba".
Shi ma ministan harkokin wajen Isra'ila mai suna Israel Katz ya bayyana ma kafar yaɗa labarai ta N12 channel cewa akwai Munafunci a cikin umarnin kamun Netanyahu da sauran mutum biyun, sai dai ya bayyana cewa idan ta kama za su daina fita cikin kasar domin kauce ma kamun.
A wani rahoto da Reuters suka wallafa a ranar asabar sun bayyana yadda wani jami'in gwamnatin Amurka yake shawartar sakataren harkokin kasashen waje Antony Blinken kan cewa lallai basu samu wata hujja da zata tabbatar da cewa Isra'ila tana bin dokokin da kare hakkokin ɗan Adam wajen amfani da makaman da Amurka ke bata ba.
0 Comments