Daga - Mahadi Tukur Almizan
Rundunar sojin ta Yemen ta bayyana cewa ta hari jiragen dakon kaya na ƴan kasuwa da suka nufi tashar jiragen ruwan Isra'ila ta Eilat.
Rundunar sojin ta Yeman ta fitar da sanarwa a jiya Laraba cewa ta farmaki jirage biyu a Red Sea ciki har da jirgin yaƙin Amurka 'US Destroyer Warship'.
"Ɓangaren sojin ruwa na Yemen sun ƙaddamar da hari kan jirgin yaƙin Amurka USS Mason' a Red Sea, rundunar ta hari jirgin da missiles" cewar mai magana da yawun rundunar sojin ta Yemen Birgediya Yahya Saree a lokacin da yake tabbatar da nasarar harar jirgin na Amurka a gidan talabijin.
بيان القوات المسلحة اليمنية بشأن استهداف المدمرة الأمريكية "ميسون" في البحر الأحمر، وكذا استهداف السفينة "Destiny " في البحر الأحمر أيضا بعد انتهاكها قرار حظر مرور السفن إلى موانئ فلسطين المحتلة. 15_05_2024م
— العميد يحيى سريع (@army21ye) May 15, 2024
pic.twitter.com/9aMnDxtO52
Saree ya kara tabbatar da matsayar sojin na Yemen cewa ba za su dakatar da hare haren nan ba har sai Isra'ila ta dakatar da hare hare kan al'ummar Palestinu.
0 Comments