Daga - Mahadi Tukur Almizan
Da ranar jiya Litinin ne dai mummunan labarin faɗuwar jirgin sama wanda shugaban kasar Iran Ibraheem Ra'isi da ƴan rakiyar sa ya karade kafafen sada zumunta.
Kafafen yaɗa labarai na cikin gida na kasar Iran sun bayyana cewa jirgin yayi saukar dole ne ba hatsari yayi ba, yayi saukar dolen ne sakamakon rashin kyawun yanayi, sai dai jirgin ya sauka a wurin da ba a sani ba a tsakanin tsaunuka.
#Iranian rescue teams have reached the site of the wreckage of the Iranian president's helicopter and the accompanying delegation. An official announcement regarding the final update on the fate of the helicopter will be issued shortly.#Iran pic.twitter.com/ZbiVT6udDU
— Al Mayadeen English (@MayadeenEnglish) May 20, 2024
Wannan ya sabbaba wahalar da aka sha wajen neman inda jirgin ya faɗi, masu agajin gaggawa suka garzaya yankin da lamarin ya faru domin laluben jirgin kamar yadda ministan harkokin cikin gida na Iran Ahmad Vahidi ya sanar da manema labarai a jiyan, tun da rana ake laluben har zuwa safiyar yau Litinin.
Tun bayan faruwar lamarin da al'ummar kasar Iran sun shiga cikin yanayi na kaɗuwa, inda akayi ta addu'o'i musamman a haramin ma'asumai, wannan yasa Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran yin kalaman kira ga al'ummar ƙasa su kwantar da hankalin su sannan kuma su cigaba da addu'o'i.
Jirgin yana ɗauke da Shugaban ƙasa Ibrahim Ra'isi, Ministan harkokin wajen Iran Amir Abdollahian, Limamin juma'a na Tabriz da kuma wani mutum daya.
Lamarin ya faru ne a kusa da bidar Iran da Azrabijan a lokacin da suke kan hanyar su ta dawowa daga Azerbaijan domin buɗe wani aikin haɗaka na gina Dam mai suna 'Qiz Qalasi' a iyakar ƙasar Iran da Azerbaijan ɗin wanda ya damu halartar shugaban Azerbaijan ɗin Ilham Aliyev.
An samu tabbacin Shahadar Ra'isi da tawagarsa daga bakin mataimakin shugaban kasar ta Iran Mohsen Mansouri a wata sanarwa da ya fitar a kafafen sada zumunta da kuma gidajen Talabijin.
Hotuna daga inda lamarin ya faru sun nuna yadda jirgin yayi kaca-kaca kuma ya kone sai ɗan abinda ya ragu.
Jirgin dai kirar Amurka ne mai suna "Subaru Bell 412" kamar yadda kafar yaɗa labarai ta kasar Iran IRNA ta tabbatar,
Wannan jirgi dai jami'an ƴan sanda, hukumar agaji duk suna amfani dashi duba da takardun irin wannan jirgi na hukumar 'European Union Aviation Safety Agency' wannan jirgin yana ɗaukar mutum 15 har da mai tuƙi.
Shugaban hukumar bada agaji ta Red Crescent Pirhossain Kolivand ya bayyana ma manema labarai cewa ko a lokacin da suka isa wajen da jirgin ya faɗi babu alamar wani daga cikin waɗanda ke jirgin na da rai.
Tun bayan faruwar lamarin dai kasashe da dama sun nuna damuwar su da kuma yunkurin bada agaji wajen laluben jirgin kamar Syria, Iraq, Azerbaijan, China da Russia.
Irin wannan lamari dai ya taɓa faruwa da irin wannan jirgi a shekarar 2018 a Iran inda ya kashe mutum 4.
0 Comments