Daga - Yusuf Kabir
Bayan samun nasarar juyin,a ranar 2 ga watan Ordebehesht (22 ga Afrilun 1980) wasu jiragen yakin Amurka sun sauka a tsohon sansanin sojin Amurkan da ke Hamadan Gabashin Iran domin su yi ruwan Bama-bamai a gidan Imam,amma Allah ya hana afkuwar hakan.Wannan lamarin ya faru ne a sakamakon guguwar iska mai dauke da rairayi da suka hana su tashi hakan ya sa shirin ya wargaje.Faruwar hakan ke da wuya,Shugaban kasar Amurka na lokacin Jimmiy Carter ya bayar da umarnin dakatar da shirin da gaggawa.Bayan lamarin ya faru hakika manazarta da fitattun 'yan Jarida sun rubuta Littafai dangane da manufar da Amurka ta so ta cimma a lokacin da ta so aiwatar da harin.
A ranar 30 ga watan Khordad shekara ta 1360 ne dai 'yan kungiyar munafukai suka gudanar da zanga-zanga a Tehran da takai ga zubar jini da haifar da tashin hankali .Bincike ya nuna hannun Amurka da kawayenta wajen haifar da boren.
YAKIN IRAKI DA IRAN NA SHEKARU 8.
Bayan rashin samun nasarar kifar da jaririyar hukumar Musulunci da Amurka da kawayeta suka yi sai suka bai wa Saddam Husaini Tikriti domin ya rusa juyin.Bugu da kari sun kara jin haushin rashin kwato 'yan leken asirin Amurka da suka yi.Wannan dalilin da wadansu na cikin dalilin da ya sa Amurka ta zabi Saddam ta ba shi miyagun makamai domin kaddamar da yaki a kan juyin Iran din.Wannan zaben da aka yi wa Iraki don yakar Iran din ba wai ya zo haka ba ne kawai,a'a ya zo ne saboda kasar Iraki a lokacin babbar kawar tarayyar Sobiyeti da kasashen gabashi ce,don haka ba makawa idan har ta kaddamar da yaki a kan Iran za su goya mata baya.
Sojojin Iraki dai sun fara kai miyagun hare-hare zuwa arewacin kasar Iran wanda ya kai kimanin kilomita 1280.Kafin wadannan hare-haren dai,kasar Iraki ta gama shirya makamanta saboda taimakon da take samu daga kasar Faransa,Amurka,Ingila.
Lallai a lokacin Sojojin Iran ba su da shiri cikakke domin fuskantar hare-haren sojojin Saddam;A haka dai suka ci gaba da kare kasarsu.A gefe guda kuma dakarun kare juyin Iran (IRGC) ba a jima da kafa su ba,sannan ba su yi karfi yadda ya kamata ba.
Bayan wasu kwanaki da fara yakin,Imam Khumaini ya gana da jakadun kasashe musulmi da ke Tehran in da ya shaida musu cewa:"Hakika mu muna kare Musulunci ne,masu kare Musulunci kuwa suna sadaukar da rayukansu,dukiya da masoyansu saboda shi,kuma ba za su taba juyawa da baya daga hakan ba."
Ganin yadda yakin yake gudanuwa,sai Imam Khumaini ya fitar da fatawar kariya ga kai hakan ya sa aka samu sojojin sa kai (Basij).Wannan kiran na samar da dakaru miliyan 20 ya samu gagarumar karba musamman daga matasa.Samun miliyoyin matasa da suke sadaukarwa wajen kare kasarsu,hakan ya bakanta ran Amurka da kawayenta.A lokacin sun ci gaba bai wa Saddam miyagun makamai cikin su kuwa har da makami mai linzami kirar Super-standard aircraft kirar Faransa.A daidai lokacin Amurka ta tilastawa kasashen Saudiyya,Kuwaiti, daukar nauyin kudaden da Saddam yake kashewa a yakin.A cikin manyan ta'addancin da Saddam ya aiwatar har da harbo jirgin fasinjan Iran mai lamba ta 655 a ranar 12 ga watan Tir 1367 (3 ga watan Yuli 1988) da ya yi sanadiyyar rasuwar yara da mata 290.
Bugu da kari Saddam ya sake kai hari ga garin Halabja da ke Iran in da mutane sama da dubu 5 suka rasu a sakamakon shakar iska mai guba da ke tattare da makamin da ya harba musu.
A gefe guda kuma duk da yanayin hare-haren Saddam yake kaiwa Iran,amma Imam ya ci gaba da gina tattare da gyara barnar da Shah ya aiwatar a gwamatinsa a Birane da kauyukan Iran din.Manyan almajiransa irin su Ayatullahi Khamne'i (Shugaban kasar lokacin) Injiniya Mir Husaini Musawi (Priminista),Ali Akbar Hashimi Rafsanjani (Shugaban majalissar shawarar Musulunci),Ayatullahi Muwasawi Ardabili (Shugaban ma'aikatar shari'a),Hujjatul Islam Haj Sayyid Ahmad Khumaini sun kasance wadanda suka yi matukar sadaukarwa a kan hakan.Wannan yakin dai ya kai ga samun Shahidai sama da miliyan 2.Nasara dai ta kasance tattare da Imam Khumaini bisa tallafi da taimako na Allah.
A ranar 24 ga watan Fabrairu 1989,a kokarin daidaitawa da dukkanin bangarorin gwamnatin Musulunci ta Iran,Imam ya yi umarni da kafa kwamatin kwararru da zai sake duba tsarin mulki.
A ranar 11 ga watan Dey 1367 (4 ga Janairu 1988),Imam ya aika wata wasika ga shugaban tarayyar Sobiyeti Mikhail Gorbachev dangane da makomar kwaminisanci a yayin da yake cewa:"Daga yanzu kwaminisanci kam sai dai a neme shi a ma'anadar kayayyakin tarihin siyasar duniya."(Ayatullahi Jawad Amuli ne ya jagoranci tawagar da Imam ya aika ga Gorbachev).A cikin sashen wasikar Imam yana cewa:"Asalin matsalar kasarka ba ta mallakar dukiya ko tattalin arziki ko 'yanci ba ce.Matsalarku ta rashin imani da Allah ne.Ita ce kuma wannan matsalar da ta kai Yammacin Turai ga lalacewa da karewa da hasara." Gorbachev dai ya aiko Eduard Shevardnaze da amsar wasikarsa ga Imam Khumaini.
A ranar 2 ga watan mayu 1979 ne dai kungiyar 'yan ta'adda ta "Furkan" ta kashe fitaccen Malamin nan,sannanen mufakkirin nan Ayatullahi Murtadhal Muddahari tare da Ayatullahi Kadiy Tabtaba'iy wanda hakan ba karamar jarabawa ba ce ga Imam da kuma al'ummar musulmi na duniya.Ayatullahi Maddahari dai Imam ya rike shi tamkar dansa mun taba kawo tarihinsa a filin nan a watannin baya.
A ranar 14 ga watan Janairu 1981 Imam Khumaini ya yi rijistar abubuwan da ya mallaka da mika bayanan hakan ga kotin koli kamar yadda doka ta tanada.Sayyid Ahmad Khumaini bayan rasuwar Imam ya aikawa gidajen Jaridu da Talabijin kwafen takardar domin su yadawa al'umma.
An buga wannan rubutun a shafin MADUBI na Jaridar Almizan a tsakanin watanin Rajab/Sha'aban na shekarar 1444.Mun sake bijiro da shi ne domin tunatar da juna irin jiga-jigan juyin da aka kashe hakan kuma bai rusa juyin ba,illa ma ya kara bunkasa ne.
kabiruusuf533@gmail.com.09063281016.
0 Comments