Wata Ƙungiyar Masu Kutse (Hackers) Ta Yi Kutse A Na'urorin Ɗab'i (Printers) Dubu 30 A Turai, Sun Gurza Takaddun Goyon Bayan Palasɗinawa.


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Ƙungiyar da ta baiwa kanta sunan sojan Amurka da ya kona kanshi kwanakin baya domin nuna goyon bayan shi ga al'ummar Palestinu.

Ƙungiyar 'Bushnell's Men' sunyi nasarar yin kutse a na'urorin gurza takardu wato 'Printer' har guda dubu 30 a Turai a kokarin su na bayyana goyon baya ga al'ummar Palestinu.

Wannan ƙungiya ta masu kutsen sun samu ƙwarin gwuiwa ne daga abinda jami'in sojin saman Amurka mai suna Aaron Bushnell yayi na ƙona kanshi a watan February domin nuna goyon baya ga al'ummar Palestinu da kuma nuna adawa da taimakon da kasar shi ta Amurka ke baiwa Isra'ila.


Ƙungiyar ta 'Bushnell's Men's sun wallafa wani saƙo a zauren su na Telegram a ranar 14 ga watan March, inda suka bayyana cewa membobin ƙungiyar sun zabi hanyar yin kutse a na'urorin Printing guda dubu 30 a faɗin duniya domin fallasa kisan kiyashin Isra'ila kan al'ummar Palestinu.

A sakon da suka wallafa a zauren nasu sun yi kira cewa "Muna kiran duk wani mai neman gaskiya ya yi musharaka damu wajen wannan aiki, babban burin mu shine mu isar da saƙon marigayi Aaron na ganin an dakatar da kisan gillar da ake yi a Gaza, marigayi Aaron ya sadaukar da rayuwar shi a maimakon sauran sojojin Amurka da ake tilasta ma kashe kashe al'ummar Gaza, Aaron baiyi mutuwar banza ba domin mutuwar shi ta karfafi mutane da dama domin su yaƙi rashin gaskiya da rashin adalci".


A ranar 25 ga watan February Aaron Bushnell mai kimanin shekaru 25 da yake aiki a matsayin sojin saman Amurka ya cinnama kanshi wuta a gaban Ofishin jakadancin Isra'ila dake birnin Washington DC na Amurka  yayin da yake yima kanshi bidiyon kaitsaye ta Twitch , yayi bidiyon yayin da take tafiya zuwa ofishin jakadancin na Isra'ila yana mai faɗin cewa "Ina  zanga zangar adawa da halin da ƴan mamata suka jefa al'ummar Palestinu ne" a karshe ya rufe da cewa bazai taba Kasancewa daga cikin masu wannan aika aikar ba" sannan ya watsa ma kanshi makamashi ya cinna ma kanshi wuta.

A ranar 17 ga watan March ƴan ƙungiyar ta 'Bushnell's Men's' suka wallafa wasu takardu da suka nuna yadda suka yi nasarar yin kutsen cikin nasara a na'urar Printing ta jami'ar Goethe dake Frankfurt ta ƙasar Germany.


Hakanan a washe garin ranar sun wallafa wasu takardu masu ɗauke da hotunan marigayi Bushnell da ƙiyasin adadin Falasɗinawa da aka kashe da wadanda aka jima raunuka da wadanda suka rasa muhallan su sakamakon Bama Baman  Isra'ila da suka sauka a gidajen su a Gaza.


Hakan a ranar 1 ga watan May da muke ciki sun wallafa wasu takardu cikin yaren 'Hebrew' na Isra'ila suna masu bayyana irin asarar da wannan yaƙin ya jawo ma Isra'ila kamar adadin sojojin Isra'ila da suka mutu, adadin Isra'ilawan  da Hamas ta kama da kuma adadin Isra'ilawan da yaƙin ya raba da muhallan su.


Ƙungiyar ta wallafa wani sako a zauren ta na Telegram inda ta bayyana cewa "Mun aika ma al'ummar Isra'ila saƙo ta hanyar na'urorin Printing mun bayyana masu gaskiya mai ɗaci, domin su gane cewa wannan yaƙin zai amfani Netanyahu ne kaɗai, su kuma al'ummar Isra'ila wahalar ce kawai tasu".


Hakanan kuma sun bayyana cewa sun tura alkaluman ta'addancin Isra'ila kan al'ummar Palestinu zuwa ga al'ummar Turai ta hanyar na'urorin Printers"


Domin tabbatar da cewa sakon nin su suna isa ƙungiyar ta wallafa wani bidiyon da CCTV Camera ta naɗa da ya nuna wasu mata biyu suna duba takardun yayin da Printer take gurzasu a jami'ar Texas.

Bayan Qarin Bushnell ya kashe kanshi ƙungiyar Mujahidai ta Hamas ta jinjina mashi inda ta bayyana shi a matsayin jarumin da ya nuna darajar ɗan Adam.

Post a Comment

0 Comments