Zuwan Sayyid Zakzaky (H) Iraq Da Ganawa Da Ɗalibai.


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Jagoran harkar Musulunci a Najeriya Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ya yo tafiya zuwa kasar Iraqi da ke gabas ta tsakiya, Sayyid Zakzaky (H) yayi tafiyar ne domin halartar taron majalisar ta 'Majma'ut-taqarib bainal mazahib' da ya gudana a ƙasar ta Iraqi.

A ranar Alhamis 9 ga watan May da muke ciki ne shafin Sayyid Zakzaky (H) ya fitar da sanarwar halartar taron.

"Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya halarci taron ƙasa da ƙasa kashi na 2 don nuna goyon baya ga Al'ummar Falastinu mai taken "Ɗufanul Aqsa" da kungiyar samar da kusanci tsakanin mazhabobin musulunci  da ake kira (Majma'a Taqrib bainal mazahib) ta shirya a ranar laraba a birnin Bagadaza, ƙasar Iraki"

Manyan malamai daga mazhabobi daban daban na musulunci suka halarci taron.


GANAWAR JAGORA DA ƊALIBAI.

A jiya Juma'a da dare kuma Jagora Sayyid Zakzaky (H) ya gana da ƴan uwa maza da mata ɗalibai ƴan Najeriya dake karatu a ƙasar ta Iraqi.

Ganawar ta gudana ne a Maƙaamu Ameeril Muminin dake birnin Najaf na kasar ta Iraqi.

A lokacin ganawar Sayyid Zakzaky ya ja hankalin ɗaliban mahalarta ganawar ga wani yanki na jawabin nashi.

"Masu karatun Hawza, kunzo ɗiban ruwa ne, domin ku kawo gida a sha, ana nan gida ana jiran ku da ƙishi, kada kuzo ku shantake a bakin rafin ku sha ku kaɗai. Idan an ɗebo a kawo gida, akwai mabuƙata.

Hakanan a ranar Larabar Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) tare da majalisar ƙoli ta Majma'ut Taqrib bainal mazahib sun gana da firaministan ƙasar Iraq,  Muhammad Shi'a AlSudani kamar yadda zaku gani cikin bidiyon dake ƙasa

Wannan shine karo na biyu da majalisar ƙoli ta "Majma'ut-taqarib bainal mazahib" ta gudanar da taro a wannan shekarar a karon farko ta gudanar da makamancin wannan taro a ƙasar Iran a ranar Lahadi 14 ga watan January wanda ya samu halartar Malaman bangarorin Musulunci daban daban ciki har da Shaikh Mahmoud Ahmad Gumi daga nan gida Najeriya da kuma wani Shehin Malami daga ƙasar Nijar.




Post a Comment

0 Comments