A Hukumance Amurka Ta Tabbatar Cewa Zata Taimaka Ma Isra'ila Idan Yaƙi Ya Ɓarke Tsakanin Ta Da Hezbollah.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Manyan jami'an fadar mulki ta White House sun tabbatar ma takwarorin su na Isra'ila cewa Amurka zata taimakawa Isra'ila da makamai idan yaƙi ya barke tsakanin su da Lebanon, amma dai Amurka ba zata tura sojojin ta ba.


Manyan jami'an gwamnatin ta Amurka sun bayyana ma jami'an gwamnatin Tel Aviv cewa  Amurka ta shirya tsaf domin taimaka ma Isra'ila idan har yaƙin ya barke kamar yadda kafar yaɗa labarai ta CNN ta wallafa.


Ɗaya daga cikin jami'an gwamnatin Amurka ya tabbatar ma CNN cewa manyan jami'an fadar mulkin Amurka sun baiwa wakilan da Isra'ila ta aiko zuwa Amurka wannan tabbacin ne  a wannan makon.



Manyan Jami'an Isra'ila da Amirka  da suka gana  sun haɗa da Ministan Strategic Affairs na Isra'ila Ron Darmer, National Security Adviser na Isra'ila Tzachi Hanegbi sai bangaren Amurka kuma akwai National Security Adviser Jack Sullivan da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da kuma White House middle East Affairs Co-ordinator Brett McGurk.


Wannan tabbaci da Amurka ta baiwa Isra'ila gaba da gaba ya zo ne a daidai lokacin da lamurra suka kazanta tsakanin Isra'ila da ƴan Muqawama na Lebanon, a cikin ƴan makonnin nan Hezbollah ta kara ƙaimi wajen kaima Isra'ila hare hare a bodar ta da Lebanon.


A gefe guda kuma Isra'ila tayi barazanar kai hare hare cikin Lebanon har kan unguwannin farar hula harma da babban birnin ƙasar ta Lebanon Beirut.


Daga cikin abinda ya fusata Isra'ila har da gazawar su wajen samar da aminci ga ƴan kama wuri zauna da hare haren Hezbollah suka kora daga matsugannan kudanci.


Sai dai Amurka ta bayyana a fili cewa zata samar ma Isra'ila duk wani nau'in taimako na tsaro da take buƙata amma ba zata tura sojojin ta ba.



Sai dai a lokaci guda kuma Amurka ta gargadi Isra'ila cewa idan yaƙi ya barke tsakanin ta da Hezbollah lallai hare hare na Hezbollah za su gajiyar da Iron Dome ɗin Isra'ila ba zai iya jure dubunnan rokoki da missiles ɗin da Hezbollah zata harbo ba.


Sai dai zuwa yanzu ba a gama tabbatar da ko Isra'ila zata iya wannan yaƙi da Hezbollah ba kasantuwar karancin dakarun da take fuskanta wanda ƙwamin ta da Hamas ya haifar inda dakarun na Hamas suka kashe adadi mai yawa na sojin na Isra'ila kuma suka raunata wani adadi mai yawa da raunuka na zahiri da na ƙwaƙwalwa.

Post a Comment

0 Comments