A Karon Farko Ƴan Muqawama Na Iraqi Da Yemen Sun Yi Haɗaka Sun Hari Jiragen Dakon Makamai Zuwa Isra'ila.

Daga - Mahadi Tukur Almizan

A ranar Alhamis 6 ga watan June dakarun Ansarullah na Yemen sunyi haɗaka wajen kai hare hare biyu a jere zuwa tashar jiragen ruwa ta Haifa.


Wannan hare hare tsakanin "Islamic Resistance Of Iraqi" da dakarun sojin Yemen ta biyo bayan makonni biyu da sanarwar haɗaka a tsakanin ƙungiyoyin biyu.

Birgediya Janar Yahya Saree ya bayyana cewa "Haɗakar rundunonin biyu sun kai hari ne kan jiragen ruwa biyu masu ɗauke da kayan soji a tashar jiragen ruwa ta haifa, wanda suka karya dokar rundunonin ta hana jirage shiga tashar ta haifa". Saree yayi wannan sanarwa a ranar Alhamis.

Ya kara da cewa "Sun yi amfani da Drones wajen kai waɗannan hare hare kuma sun samu target ɗin su cikin nasara".


A cikin watan da ya gabata ne shugaban ƙungiyar Ansarullah ta Yemen Sayyid AbdulMalik Alhouthi ya tattauna da shugaban rundunar Kata'ib Hezbollah ta Iraqi Abu Hussein al-Hamidawi, a wanna tattaunawar ne shugabannin biyu suka yi matsayar yin haɗaka wajen kai ma Isra'ila hare hare.

Post a Comment

0 Comments