Daga - Mahadi Tukur Almizan
Jami'an ƴan sandan ƙasar Kenya sun kashe mutum 1 tare da raunata aƙalla mutum 200 a wata zanga zanga da aka gudanar a faɗin ƙasar domin nuna adawa da kudirin gwamnati na sar da Dalar Amurka $2.7billion ta hanyar karin haraji.
Jami'an ƴan sandan sun harba barkonon tsohuwa da fesa ruwan zafi domin tarwatsa zanga zangar a Nairobi babban birnin ƙasar ta Kenya, zaku iya kallo cikin bidiyon dake ƙasa
@LastWeekTonight
— Muleh (@mulecular) June 20, 2024
Hey John Oliver!
Scenes from Tuesday and Today in Nairobi
All this because we don't want to be overtaxed to death. Taxing cancer and periods, 800M confidential fund
Today we had nation wide protests
#REJECTFİNANCEBİLL2024 #RejectFinaneBill2024 pic.twitter.com/UTOJDPJIxO
Zanga Zangar dai haɗaka ce tsakanin wasu kungiyoyin fafutuka guda biyar ciki har da 'Amnesty International, da Kenya Medical Association.
Jami'an ƴan sandan sun harba harsashi mai rai wanda ya kashe mutum ɗaya kuma wasu suka samu raunuka, sannan kuma sun kama sama da mutum 100 cikin masu zanga zangar a faɗin Kenya.
An tabbatar da hukumar ta ƴan sanda ta tattara bayanan wanda ya mutum, namiji ne mai suna Rex Kanyike ɗan kimanin shekaru 29, kuma cikin waɗanda suka samu raunuka har da jam'i'an ƴan sanda.
Mahaifiyar wanda aka kashe ɗin mai suna Gillian Munyau ta bayyana cewa wani abokin ɗan nata da aka kashe ya bata labarin cewa wani ɗan sanda cikin farin kaya ne ya harbe ɗan nata yayin da suke guduwa ma barkonon tsohuwa.
Mahaifiyar mamacin ta bayyana ma kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa " Me zai sa ayi amfani da harsashi me rai kan masu neman ƴanci, shin yana ɗauke da makami ne? Inda yana ɗauke da makami ne ƙila mu iya fahimtar dalilin harbe shi, kawai yana tafiya ne tare da abokan shi? Ta yi wannan magana ne a bakin kofar Mutuary da aka ajiye ɗanta lokacin da take karɓar gawar shi.
0 Comments