Daga - Mahadi Tukur Almizan
Wani mutum ya buɗe wuta kan mai uwa da wabi a gaban Ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Beirut na ƙasar Lebanon.
Ofishin jakadancin na Amurka na unguwar Awkar da ke birnin Beirut babban birnin ƙasar ta Lebanon.
A wani sako da ofishin jakadancin na Amurka ya wallafa a shafin X (Twitter), ofishin ya bayyana cewa " Da misalin ƙarfe 8:34 na safiyar yau Laraba wani mahari ya buɗe wuta a mashigar ofishin jakadancin na Amurka". Ofishin jakadancin ya miƙa godiya ga rundunar sojin kasar ta Lebanon bisa kokarin da suka yi na gaggawar kawo ɗauki har kuma suka yi nasarar kama maharin.
At 8:34 a.m. local time, small arms fire was reported in the vicinity of the entrance to the U.S. Embassy. Thanks to the quick reaction of the LAF, ISF, and our Embassy security team, our facility and our team are safe. Investigations are underway and we are in close contact…
— U.S. Embassy Beirut (@usembassybeirut) June 5, 2024
A wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen yada labarai ya nuna yadda maharin lokacin da yake rike da bindiga yana harbi a gaban Ofishin kafin jami'an rundunar sojin ta Lebanon su buɗe mashi wuta, sun raunata shi da harbin da suka yi mashi.
Shooting at the American embassy in Lebanon
— Sprinter infofactory (@Sprinter00000) June 5, 2024
A man shot at the security of the American embassy, and the Lebanese armed forces returned fire, wounded the attacker and he was taken into custody, according to the Lebanese army. pic.twitter.com/DGq796LGjM
Firaministan kasar Lebanon yasanar da cewa za a gudanar da cikakken bincike dangane da harin.
Wakilin kafar yaɗa labarai ta The Cradle ya bayyana cewa maharin na raye duk da harbin da sojin na Lebanon suka yi nashi kuma sojin sun ɗauke shi zuwa asibitin soji domin kulawa da lafiyar shi.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa dai mutumin ɗan kungiyar ISIS ne daga Syria, kuma ya kai harin ne domin nuna goyon bayan Palasɗinawa da kuma adawa da Amurka a bisa cigaba da taimaka ma Isra'ila a hare haren da take kaiwa kan al'ummar Palestinu.
Madogarar wadannan majiyoyi itace a ranar 28 ga watan March mai magana da yawun kungiyar ta ISIS Abu Huzaifa al-Ansari ya yi wani jawabi inda ya kirayi ƴan kungiyar da cewa sukai hari a ɗaiɗaikun su kan Amurka da sauran ƙasashen Yamma dake giya ma Isra'ila baya.
0 Comments