Bahrain Ta Nemi Shiryawa Da Iran Ta Hannun Rasha

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Jami'an masarautar Bahrain sun bayyana cewa fadar mulki ta Manama na neman shiryawa da fadar mulkin Tehran bayan rashin jituwa na tsawon shekaru a tsakanin ƙasashen biyu.

Kasar ta Bahrain ta aika da sakon neman Rasha ta shiga tsakani ta daidaita harkar diflomasiyya a tsakanin Bahrain ɗin da Iran kamar yadda kafafen yada labaran Iran suka labarto mai baiwa shugaban kasa shawara Muhammad Jamshidi yana faɗi.

Rahoton ya fito ne a ranar juma'a bayan sanarwa mabanbanta da suka fito daga jami'an gwamnatin Bahrain na buɗe kofar daidaita rashin jituwar dake tsakanin ƙasashen biyu.


Kafafen yaɗa labarai ciki har da Press TV da Tehran Times sun wallafa rahoton da Jamshidi yake faɗin cewa "Bahrain ta turo ma Iran saƙo ta hannun kasar Rasha domin daidaita tsakanin Iran da Bahrain".

Masarautar kasar Bahrain dai ta yanke hulɗar diflomasiyya tsakanin ta da Iran ne a shekarar 2016 sakamakon samun rashin jituwa tsakanin Saudiyya da Iran.


Daga cikin abubuwan da ya tsamama alaka a tsakanin ƙasashen biyu har da zargin da Bahrain take yi ma Iran cewa akwai hannun Iran a zanga zangar adawa da gwamnati da ta kusa cinye gwamnatin a shekarar 2011.


Sarkin kasar ta Bahrain Hamad Bin Isa Al-Khalifa da kanshi yayi magana akan wannan daidaiton a lokuta mabanbanta daga ciki akwai lokacin da yayi maganar a ganawar sa da firaministan kasar China a makon da ya gabata a birnin Beijing.


Hakanan kuma a watan da ya gabata Sarkin ya bayyana cewa ƙasar shi na cigaba da kokarin kyautata alaƙa da kasar Iran a lokacin da yakai ziyara birnin Moscow a watan da ya gabata.


Hakanan kafar yaɗa labaran kasar ta Bahrain "Bahrain News Agency" ta labarto Sarkin yana cewa babu dalilin jinkirin kyautata alaƙa tsakanin ƙasashen biyu".

A watan da ya gabata Sarkin na Bahrain ya aika sakon ta'aziyyar rashin shugaba Ra'isi zuwa ga jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Sayyid Ali Khamene'i.

Sai dai a gefe guda ana ganin wannan kyautata alaƙar tsakanin Bahrain da Iran zai lalata Alaƙar dake tsakanin Bahrain da Isra'ila da kuma Amurka sakamakon kasancewar su manyan abokan adawar Iran.

A shekarar 2020 kasar Bahrain ta kulla alaka da Isra'ila ta hannun Amurka kuma shekara biyu bayan kulla wannan  alaka Bahrain ta ƙalla yarjejeniyar tsaro tsakanin ta da Isra'ila.

Hakanan kuma a baya bayan nan a  cikin watan December na shekarar da ta gabata 2023 Bahrain ta shiga ƙawancen Amurka wajen daƙile hare haren dakarun Ansarullah na Yemen kan jiragen Isra'ila a Red Sea.

Post a Comment

0 Comments