BINCIKE: Bullet Guda 335 Sojin Isra'ila Suka Zazzaga Ma Motar Da Yarinya Ƴar Shekara 6 Da Ƴan Uwanta Suke Ciki.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Bincike ya tabbatar da yadda tankar sojin Isra'ila ta kashe yarinya ƴar shekara 6 mai suna Hind Rajab


Motar sojin Isra'ila mai suke ta zazzaga ma motar da yarinyar take ciki tare da yan uwan ta bullet har guda 335, kuma suna sani cewa suna cikin motar.


Ƙwararrun masu bincike na Forensic Architecture ne suka gudanar bincike kan yadda harin ya faru kuma suka fitar da sakamakon binciina yadda motar sojin ta Isra'ila ta buɗe ma motar su Hind Hijab wuta.

An kashe Hind da yan uwan ta ne a ranar 29 ga watan January na wannan shekarar yayinda suke kokarin barin Gaza bayan da Isra'ila ta baiwa fararen hula umarnin barin Gaza, an samu gawar su ne bayan kwanaki 12 da buɗe ma motar ta su wuta.


Forensic Architecture sun nuna yadda suka samu ramukan shigar harsashi guda 335 a jikin motar ta su Hind kirar Kia Sedan.


Forensic Architecture sun yi haɗin gwuiwa da ƴan jaridar Earshot da Al-Jazeera Fault Line, a binciken sun gano cewa wasu jami'an bada agajin gaggawa na Palestine Crescent Society sun yi kokarin ceto Hind Rajab a kokarin hakan suma sojojin na Isra'ila suka yi amfani da motar soji mai sulke suka harbe su.


A lokacin da abun ya faru ya dauki hankalin duniya musamman jin sautin wayar da gwaggon Hind ta yi, ta na kiran a kawo masu ɗauki, gwaggon Hind mai suna Layan Hamadan mai kimanin shekaru 15.

Layan ta kira jami'an Palestine Crescent Society ne lokacin manyan su dake cikin motar sun riga sun mutu.


"Sun buɗe mana wuta, ga tankar su nan kusa da ni, muna cikin motar" waɗannan sune kalaman Layan  lokacin da ta kira wayar.


Layan ta cigaba da kuwwa a wayar na tsawon sakwanni 20 a wayar.


A lokacin da Layan take wayar anji fitar adadin harsashi 64 cikin sakwan 6, hakan ya nuna fire range na harsashi 750-900 a duk minti ɗaya.


Bayan faruwar lamarin Isra'ila tayi kokarin bayyana cewa tankokin sojin ta basa a yankin da aka buɗe ma Hind da ƴan uwan ta wuta, wai harbin dakarun Hamas ne ya same su.


Sai dai Forensic Architecture sun binciko fire range da suka ji a kiran wayar Layan ya zarce na AK-47 wanda sune bindigun da dakarun Hamas suke amfani da su.


Duba da karar tafiyar bullet ɗin da gudun shi da kuma karar fitar shi daga bakin bindiga Earshot sun suna cewa tazarar dake tsakanin motar su Layan da Tankar dake harbin su baiwuce meter 13 zuwa 23 ba.


"Da wannan tazarar ta meter 13 zuwa 23 babu makawa mai yin harbin yana ganin cewa farar hula ne da ƙananan yara a cikin motar" a cewar Forensic Architecture




Ma'aikatan Palestine Crescent Society biyu da aka kashe a lokacin da suka je kai ma Layan ɗauki sune Yusuf al-Zeino da Ahmad al-Madhoun, a lokacin da suka nufi wurin Layan ce kawai ke da rai a cikin motar sauran mutanen duk sun mutu.


Forensic Architecture sun bayyana cewa Ambulance ɗin da ma'aikatan agajin suke ciki  an tarwatsa ta da 120mm M830A1 High Explosive Anti Tank Multi Purpose Tracer (Heat-MP-T), Forensic Architecture sun tabbatar da cewa Tankar sojin Isra'ila ce ta tarwatsa Ambulance ɗin.

Post a Comment

0 Comments