Colombia Zata Kula Da Lafiyar Yaran Palasɗinawa Masu Raunuka.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Asibitin sojin kasar Colombia zata karbi Ya Palasɗinawa da suka tsira da  raunuka sakamakon hare haren Isra'ila a Gaza kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Colombia ta sanar a jiya Alhamis.

A cikin sanarwar mataimakiyar ministan harkokin wajen kasar Elizabeth Taylor Jay ta bayyana cewa Yaran zasu zo ne da rakiyar mahaifan su domin kulawa da lafiyar su, sai dai bata bayyana adadin Yaran da zasu karɓa ba da kuma lokacin da za su zo kasar da lokacin da zasu ɗauka suna zaune a kasar ta Colombia ba.

Elizabeth ta bayyana cewa ta bayyana cewa likitocin asibitin sojin sun gama shirya wa tsaf domin karbar Yaran.



Colombia ta bi sahun kasashen da suka tallafa wa Palasɗinawa ta fuskar kula da lafiya kamar kasar Germany, Jordan da haɗaddiyar daular Larabawa sai dai abinda ya banbanta Colombia da wadannan kasashen shine yanke alaka da Isra'ila.

A ranar asabar ɗin da ta gabata ne shugaban kasar ta Colombia Gustavo Petro ta sanar da dakatar da safarar Coal zuwa Isra'ila, ya tabbatar da cewa wannan dakatarwar zata cigaba har sai Isra'ila ta dakatar da kisan kare dangi kan al'ummar Palestinu.

Acikin watan March Gustavo ya gargaɗi Isra'ila cewa Indai har bata bada hadin kai ga yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza na kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya ba, to Colombia zata yanke alaƙar diflomasiyya da Tel Aviv.

Aranar 1 ga watan May ne dai Gustavo ya bayyana cewa zai datse alaƙar diflomasiyya tsakanin Colombia da Isra'ila bisa kisan kiyashin da take aikatawa a Gaza wanda yayi sanadiyyar rasa rayukan aƙalla mutum 37,232 da raunata mutum 85,037.

Hakanan kuma Gustavo ya kirayi kotun ICC ta gaggauta sauraren karar da South Africa ta shigar kan Isra'ila a lokacin da aka shigar da karar.

Hakanan kuma a cikin watan April kasar Colombia ta yi kira ga dukkanin ƙasashen kwamitin hanawa afkuwar kisan kiyashi da hukunta duk ƙasar da ta aikata cewa su marawa South Africa baya a karar da ta shigar da Isra'ila kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC).

Hakanan a cikin watan January na wannan shekarar Gustavo ya kira da a baiwa lauyoyin South Africa da suka shigar da karar Isra'ila Lambar girmamawa ta zaman lafiya.

Post a Comment

0 Comments