Daga - Mahadi Tukur Almizan
A ranar Laraba ne shugaban tsibirin Cyprus Nikos Christodoulides ya mayarda martani ga jan kunnen da shugaban Hezbollah Sayyid Hassan Nasrallah yayi masu.
Nikos ya bayyana cewa Cyprus ba ta da hannu kuma ba zata saka hannu a rikicin dake tsakanin Lebanon da Isra'ila ba, "Mun gwammaci tsayawa bangaren samar da daidaito a tsakani fiye da kasancewa bangaren matsalar".
Maganar gaskiya duk da wannan barrantar da Cyprus tayi akwai dalilai da suka nuna hannun ta wajen taimakon Isra'ila wajen yakar Lebanon, domin kuwa Cyprus ta baiwa Isra'ila wajen da tayi Atisaye domin yakar Lebanon a lokuta mabanbanta daga ciki akwai wanda kafar yaɗa labarai ta Isra'ila ta wallafa dakanta.
A ranar 2 ga watan June ma shekarar 2022 jaridar "The Times Of Israel" ta wallafa wata maƙala mai taken "I'm Cyprus, IDF runs drills for potential war with Hezbollah, Lebanon ground assault".
Zaku iya karantawa anan 👉🏽 https://www.timesofisrael.com/in-cyprus-idf-runs-drills-for-potential-war-with-hezbollah-lebanon-ground-assault/
Hakanan kuma kafar yaɗa labaran Isra'ila ta i24News ta wallafa wani faifain bidiyo da ya nuna yadda Atisayen sojin na Isra'ila ya gudana a tsibirin na Cyprus, kafar yaɗa labaran ta wallafa bidiyon ne a YouTube inda ta yi mashi taken "Israel Defense Forces carries out drills on Cyprus simulating war on Lebanon" zaku iya kallon Bidiyon anan kasa 👇
Hakanan kafar yaɗa labarai ta Haaretz ta wallafa wani rahoto da ya nuna yadda Isra'ila ta gudanar da Atisaye A Cyprus ɗin a mabanbantan lokuta
With the largest number of troops ever sent abroad, the IDF simulated military activity in 'enemy territory' in the city of Paphos. Israel caps massive war games in #Cyprus simulating #Lebanon war.
— Elijah J. Magnier 🇪🇺 (@ejmalrai) June 20, 2024
https://t.co/VmqE41wa8L
Hakanan shafin rundunar sojin Isra'ila IDF na Twitter ya taɓa wallafa bidiyon dakarun sojin Commando Brigade Egoz Unit na Isra'ila suna Atisaye a Cyprus domin yakar Lebanon
The Commando Brigade's Egoz Unit carried out a special exercise in Cyprus. Here's what it looked like. pic.twitter.com/2cMGvUPxvZ
— Israel Defense Forces (@IDF) June 15, 2017
Wannan barrantar da shugaban kasar ta Cyprus yayi zai iya zama wani taku na diflomasiyya da ya zama dole.
0 Comments