Dole Isra'ila Ta Dakatar Da Hare Hare A Rafah Ta Fuskanci Hezbollah A Arewaci, Tun Kafin Mu Rasa Abun Karewa - Shugabannin Sojin Isra'ila Sun Fara Kokawa

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Wata majiyar jami'an tsaron kasar Isra'ila sun bayyana dole ne a gaggauta ɗaukar matakin gaggawa domin Hezbollah na cigaba da ɗanɗana ma Isra'ila kuɗa ta hanyar amfani da rockets 🚀 da drones wajen babbake arewacin Isra'ila.


Wannan tasa sojojin na Isra'ila suka fara badawa shawarar dakatar da hare hare a Rafah dake kudancin Gaza cikin gaggawa domin su tarkata su koma Arewaci domin fuskantar Isra'ila kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Isra'ila (Israel's Channel 12) ta labarto a ranar juma'a 14 ga watan June.


A cikin wannan makon dai Hezbollah ta ƙaddamar da hare hare mafiya muni tundaga watan October na shekarar da ta gabata ta hanyar amfani da drones da rockets biyo bayan harin da Isra'ila ta kai da yayi sanadiyyar kashe babban Kwamandan kungiyar ta Hezbollah.


Dakarun sojin Isra'ila dake Arewaci sun bayyana cewa suna ƙoƙarin yin ɗan abinda zai rage ƙarfin hare haren Hezbollah, a kokarin rage ƙarfin hare haren na Hezbollah suna ganin lallai dole a dakatar da hare hare a Rafah a tarkato dakaru a kawo su arewaci, sojin na Isra'ila sun bayyana haka ne a lokacin zaman masu ruwa da tsaki a ranar Alhamis.


Majiyar jami'an tsaron ta bayyana ma kafar yaɗa labarai ta 'Channel 12'  cewa in har ana so ɗaruruwan mazauna iyakar ƙasar da Lebanon su iya dawowa mazaunan su to dole ne a dauki mataki na gaggawa.

Post a Comment

0 Comments