Hezbollah Na Cigaba Da Tarwatsa Iron Dome Ɗin Isra'ila.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Yanzu an wuce matakin cewa Iron Dome ɗin Isra'ila ya gaza wajen kare hare haren Hezbollah, yanzu har Iron Dome ɗin ake kaima hari.

A ranar Larabar da ta gabata rundunar Hezbollah ta hari tsarin tsaron sararin samaniyar Isra'ila da ake kira "Iron Dome Air Defence System" sun hari Iron Dome ɗin Isra'ila dake Ramot Naftali da missile.

Tashar talabijin ɗin ƙungiyar ta Hezbollah Al-Manar ce ta wallafa bidiyon harin na Hezbollah a garin na Ramot Naftali.

Faifain bidiyon ya nuna yadda missiles ɗin Hezbollah suka tarwatsa Iron Dome ɗin.

Hakanan kuma rundunar ta Hezbollah ta saki wani faifan bidiyon wani harin da ta kai kan Iron Dome ɗin a garin Zaoura dake Golan, Hezbollah ta hari wannan Iron Dome ɗin ne da Katyusha missile.

Kafar yaɗa labarai ta Al-Manar ta labarto cewa a ranar Talata Hezbollah ta kai adadin hare hare takwas, kuma ta yi ma Isra'ila ta'asa a wadannan hare hare.

Hakanan a ranar Alhamis rundunar ta Hezbollah ta kai wani kazamin hari kan sojin Isra'ila har wani sojan Isra'ila mai suna Sergeant Refael Kauders ya mutu sakamakon harin drone ɗin Hezbollah kamar yadda rundunar sojin Isra'ila ta wallafa a shafin ta.



A rahoton mai magana da rundunar sojin Isra'ila Lieutenant Colonel Peter Lerner ya bayyana cewa Sergeant Kauders mai kimanin shekaru 39 ya mutu a harin da Hezbollah ta kai garin Hurfeish dake arewacin Isra'ila.

Jaridar Israel Times ta labarto cewa harin ya raunata wasu sojoji 9, kuma a ciki akwai mai mummunan rauni.

Peter Lerner ya kara da cewa hare haren Hezbollah na kara ta'azzara kowace rana a kokarin su na raunana tsaron Isra'ila.

Post a Comment

0 Comments