Kwamitin Kula Da Zaɓe Na Ƙasar Iran Ya Fitar Da Sunayen Tsayayyun Ƴan Takara Da Za Su Kara A Zaɓen Shugaban Ƙasa.



Daga - Mahadi Tukur Almizan

Guardian Council na Iran su ke da alhakin tantance ƴan takara sannan su fitar da tsayayyun ƴan takara 6 daga cikin mutanen da suka yi rijistar tsayawa takarar.

Kafar yaɗa labaran kasar Iran IRNA ta wallafa rahotan cewa kwamitin ya fitar da sunayen mutanen da aka amince su kara a zaɓen dake tafe a ƙasar.

Mai magana da yawun hedkwatar zaɓen ƙasar Iran Mohsen Eslami ne ya fitar da sanarwae sunayen amintattun ƴan takarar da kwamitin ya tabbatar kuma ya amince da takarar su a  yau Lahadi.

Mutanen da Guardian Council suka amince da su sune; 

Mostafa Pourmohammadi tsohon ministan shari'ar kasar.

Masaoud Pezeshkian tsohon ministan lafiya na kasar.

Amirhossein Ghazizadeh shugaban gidauniyar kula da Shahidai da tsofaffin sojin kasar.

Alireza Zakani magajin garin Tehran

Saeed Jalili  tsohon wakilin Iran a tattaunawar Nukiliya

Mohammad Baqer Qalibaf shugaban majalisar kasar.

Waɗannan sune mutane 6 da aka amince da takarar su kuma sune zasu kara a zaɓen dake tafe a ranar 28 ga wannan wata na June.


Wannan zaɓe da za a yi kasar Iran shine zaɓen shugaban ƙasa karo na 14, musabbabin wannan zaɓe shine mutuwar shugaba Ra'isi da abokan tafiyar shi sakamakon faɗuwar jirgin su a ranar 19 ga watan May da ya gabata.

Post a Comment

0 Comments