Makaman Da Amurka Ta Turama Isra'ila Daga 07 October Zuwa Yau: Adadin su da nau'o'in su

 


Amurka ta aika da Bomb 27,000 zuwa Isra'ila tun daga fara kisan kiyashi a Gaza.

Daga - Mahadi Tukur Almizan


Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa rahotan yadda Amurka ta rika aikama Isra'ila makaman da take aiki da su wajen kashe al'ummar Palestinu.


Rahoton ya nuna cewa Amurka ta aika da Destructive lb Bomb guda 2,000 wanda Amurka tana sane cewa bai kamata Isra'ila ta mallaki waɗannan Bomb ɗin ba kamar yadda Reuters suka wallafa


Reuters sun bayyana cewa Amurka ta aika da Bomb ƙirar MK-84 da ake jefawa da jiragen yaƙi aƙalla guda 14,000 2000lb bombs, 6,500 500-lb, da helfire precision guided air-to-ground missiles guda 3,000, bunker buster bombs guda 1,000 da air-dropped small diameter bomb guda 2,600 da wasu kalar makamai na daban da jami'an gwamnatin Amurka ba su bayyana ba a cewar Reuters.

MK-84 Bomb


A baya bayan nan dai anji firaministan Isra'ila Benjemin Netanyahu yana ta ɓaɓatu dangane da jinkirin da aka samu na tura wasu makaman ƙirar 2000lb.

2000lb Bomb


Wani jami'in gwamnatin Amurka ya bayyana ma Axios cewa fadar gwamnatin Amurka tana zullumin sake tura Bomb ɗin ƙirar 2,000-lb zuwa Isra'ila saboda bai kamata Isra'ilar ta mallaki wannan Bomb ɗin ba, kuma suna amfani da shi a Gaza.


A watan October Isra'ila ta jefa 2,000-lb Bomb a  tsakiyar sansanin ƴan gudun hijira na Jabaliya wanda ya kashe mutum 120.



Reuters ta bayyana cewa babu alamar Amurka zata daina baiwa Isra'ila makamai duk da jinkirin da tayi na tura makamai zuwa Isra'ila a baya bayan nan.


A watan April wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam mai suna 'Euro-Med Human Rights Monitor' ta yi ƙiyasin cewa Isra'ila ta jefa aƙalla ton dubu 70 na Bomb a Gaza daga fara yaƙin zuwa watan April, wannan adadin ya zarce adadin Bomb ɗin da Amurka ta jefa a birnin Dresden na Germany da Hamburg da London a lokacin yaƙin duniya na biyu.



Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ne yayi faɗi tashin samar ma Isra'ila waɗannan makamai da suka yi sanadiyyar kashe rayukan Palasɗinawa 37,000 wanda mafi yawancin su ƙananan Yara ne da Mata.

Post a Comment

0 Comments