Mutanen Da Suka Yi Rijistar Neman Tsayawa Takarar Shugaban Kasar Iran.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Mutane da yawa ne dai suka nuna sha'awar su harma suka yi rijistar tsayawa takarar neman shugabancin kasar Iran a  zaɓen da za a gabatar domin samar da shugaban da zai maye gurbin shugaba Ra'isi da ya rasu a watan da ya gabata kamar yadda kafar yaɗa labaran kasar Iran IRNA ta labarto a ranar Lahadi 2 ga watan June.

Za a gabatar da zaɓen ne a ranar 28 ga watan June da muke ciki.

An ɗauki tsawon kwanaki 5 ana yin rijistar tsayawa takarar shugabancin kasar ne tun daga ranar 30 ga watan May zuwa Litinin 3 ga watan June, duk masu sha'awar tsayawa takarar sun hallara a hedkwatar hukumar zaben domin yin rijistar.

Dokar kasar Iran ta kayyade shekarun dan takara daga mai  shekaru 40 zuwa shekaru 75, sannan kuma dole ya kasance yana da aƙalla Master's degree, sannan kuma dole ya kasance yana da Experience ɗin aiki a gwamnatin kasar na aƙalla shekaru 4, kuma dole ne ya samu yarjewar Guardian Council mai membobi 12 na daga malaman addini.

An sanya ranar 11 ga watan June a matsayin ranar da za a bayyana sunan mutanen da aka amince su yi takara a zaɓen, wato tsayayyun ƴan takara da za a zaba a akwatunan zaɓe.


Daga wannan ranar za a cigaba da Campaign har zuwa ranar 27 ga watan June, wanda zai baiwa ƴan takarar damar yin Campaign ɗin makonni biyu kafin zaɓe.


Mutanen da suka yi rijistar tsayawa takarar sune;


Mahmoud Ahmadinajed wanda ya yi shugaban kasar Iran har karo biyu daga shekarar 2005 zuwa 2013, sai Ahmad Rasoulinejad sai tsohon dan majalisa Masaoud Pezeshkian  MP mai wakiltar birnin Tabriz.

Sai kuma Vahid Haghanian  mai taimakawa jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Sayyid Khamene'i kuma tsohon kwamandan rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran IRGC, sai Alireza Zakani magajin garin Tehran.

Sai kuma Saeed Jalili tsohon sakataren majalisar tsaron kasar Iran,  sai Mostafa Kavakebian sakataren jam'iyyar Mardomsalari.

Sai kuma Ali Larijani tsohon shugaban majalisar kasar.

Sai Habibolla Dahmardeh  gwamnan Sistan, Baluchestan, Lorestan da yankin Kerman.

Sai Mohammad Reza Mirtajodini mai taimaka ma shugaban ƙasa kan harkokin majalisar kasar kuma ya yi dan majalisa har sau biyu.

Sai Zohreh Elahian ƴar majalisar Iran a shekarar 2008 zuwa 2012 da kuma 2020 zuwa 2024.

A cikin wadannan mutanen ne dai Guardian Council za su fitar tsayayyun ƴan takara da za a zaba.

Post a Comment

0 Comments