"Operation No. 2000" : Hare Haren Hizbullah Kan Isra'ila Sun Cika Dubu 2

Daga - Mahadi Tukur Almizan

Bangaren yaɗa labarai na rundunar Hezbollah ya fitar da bidiyon hari na 2000 tun daga fara hare haren Hezbollah kan Isra'ila a kudancin Lebanon tun bayan fara Ɗuufanul Aqsa, sun cika hari na dubu 2 ne da harbo Drone ɗin Isra'ila kamar yadda faifain bidiyon ya nuna yadda dakarun rundunar ta Hezbollah suka yi ta bibiyar jirgin har zuwa lokacin da suka harboshi da missiles.

Hezbollah dai tana kai wannan hare hare ne tun farko da niyyar goyon bayan al'ummar Palestinu.

Dakarun na Hezbollah sun yi amfani da thermal Camera wajen ɗaukar yadda suka fara bibiyar jirgin na Isra'ila har zuwa lokacin da missiles ɗin da suka harba ya samu jirgin ya tarwatsa shi a saman iyakar Lebanon.

Hakanan kuma bidiyon ya nuna yadda al'ummar Lebanon suka rika ɗaukar bidiyon jirgin bayan missiles ya samu jirgin kafin ya iso ƙasa.


A ranar asabar ɗin da ta gabata ne rundunar ta Hezbollah ta fitar da sanarwar cewa sun harbi jirgin na Hermes 900 ta hanyar amfani da Surface to air missiles.

Sun Harbo jirgin a sararin samaniyar garin 'Deir Kifa".

Wannan dai bashi bane karon farko da Hezbollah ta harbo jirgin ƙirar Hermes 900, domin a cikin watan Afrilu Isra'ila ta tabbatar da cewa Hezbollah ta harbo jirgin Hermes 900 a karon farko.

Hakanan rundunar ta Hezbollah ta harbo jiragen Isra'ila mabanbanta harma kafar yaɗa labarai ta Haaretz ta tabbatar da karfin tsaron sararin samaniyar Hezbollah wanda yake bata damar harbo jiragen na Isra'ila, Hezbollah ta harbo jirgin Isra'ila ƙirar Kochav Hermes 900 kenan, zik drone, da  Hermes 450 da suka harbo a cikin  watan February.

Jirgin Hermes 900 da ake kira da Kochav ƙirar kamfanin ƙere ƙere na Isra "Elbit System" ne, an ƙirƙire shi ne domin aikin tattara bayanan sirri wato Intelligence surveillance, target acquisition, reconnaissance and aerial reconnaissance missions.

Ga taƙaitaccen bayanin wannan jirgi cikin harshen turanci.

It is a medium-altitude long-endurance (MALE) UAV with a wingspan of 15 meters (49 feet). It has a maximum takeoff weight of around 1,180 kilograms (2,600 pounds).

Operated by Squadron 166 of the Israeli Air Force, the Hermes 900 weighs 970 kg, enjoys a maximum payload weight of 350 kg, and reaches a maximum altitude of 30,000 feet.

The drone is equipped with various sensors and payloads, including electro-optical/infrared (EO/IR) cameras, synthetic aperture radar (SAR), maritime patrol radar, signals intelligence (SIGINT) systems, and electronic warfare (EW) capabilities.

The Hermes 900 enjoys a maximum flight endurance of up to 36 hours in a single sortie, allowing it to conduct long-duration missions.

Ana sarrafa wannan jirgin ne remotely daga Control Station.

Sojin saman Isra'ila sun fara aiki da Hermes 900 ne a shekarar 2012, hakanan kuma Isra'ila tayi amfani dashi wajen kai hare hare  zirin Gaza a shekarar 2014, kuma shine jirgin tattara bayanan sirri mai daraja ta biyu bayan "Heron TP" wanda ake yi ma laƙabi da Eitan.

Post a Comment

0 Comments