Rasha A Shirye Take Ta Baiwa Duk Masu Adawa Da Amurka Makamai - Cewar Dmitry Medvedev Na Rasha


Daga - Mahadi Tukur Almizan

A ranar Alhamis shugaban Rasha Dmitry Medvedev ya sanar cewa Moscow ta shirya tsaf domin ta baiwa maƙiyan Amurka makamai a matsayin martani bisa aika ma Ukraine makamai da Amurka da ƙawayenta suke.

Shugaba Putin ne ya bayyana wannan matsayar a zaman da yayi da kafafen yaɗa labarai na kasashen waje.

Dmitry ya bayyana cewa basu shirya Foreign Policy ɗin kasar ba sai yanzu da Amurka da ƴan koren su suka ɗaura aniyar aiko da kowane irin makami zuwa Ukraine domin rusa kasar Rasha ta kowace hanya, a gefe guda kuma suna yi ma duk wani mai tunanin taimakawa Rasha wajen tsaron kasar ta barazana.

"Yanzu Amurka da ƙawayenta su shirya ganin makaman Rasha a hannun wasu mutane ko ƙasashe" cewar Dmitry, ya kara da cewa " Ba zamu bayyana waɗannan mutanen ko kasashen da zamu baiwa makamai ba a halin yanzu, amma a sani cewa zasu iya kasancewa duk masu ganin Amurka da ƙawayen ta a matsayin maƙiya, ba ruwan mu da yadda duniya ke kallon su".


Amurka da ƙawayenta sun kara kaimi wajen aika makamai zuwa Ukraine ko a cikin makon nan France ta bayyana zata aika da jirgin yaƙi ƙirar "Mirage-2000" zuwa Ukraine.

Dmitry ya rufe maganar shi da cewa "Duk Wani Maƙiyin Amurka Abokin Mu Ne"



Post a Comment

0 Comments