Daga- Mahadi Tukur Almizan
A cigaba da zullumin ɓarkewar yaƙi tsakanin Hezbollah da Isra'ila rundunar ƴan Muqawama na Iraqi sun bayyana aniyar su na taimaka ma Hezbollah idan har Isra'ila ta kai ma Lebanon hari.
Mujahidan na Iraqi sun bayyana cikakken goyon bayan su Hezbollah suna masu cewa zasu taimaka da dakarun su, za su yi yaki kafaɗa da kafaɗa tare da dakarun na Hezbollah wajen yaƙar Isra'ila idan tayi gigin kawo hari Lebanon.
Kafar yaɗa labaran kasar Lebanon Al-Akhbar Newspaper ta wallafa rahoto ba tare da bayyana sunan majiyar ta ba, inda ta bayyana cewa rundunar Kata'ib Hezbollah da Harakat Hezbollah al-Nujaba dukkanin su daga Iraqi sun sanar da cewa a shirye suke tsaf domin taimaka ma Hezbollah.
Majiyar Al-Akhbar ta bayyana cewa a halin yanzu waɗannan rundunoni suna jiran amincewar Hezbollah ne kawai.
Mai magana da yaqin rundunar Kata'ib Sayyidus-Shuhada Kazim Al-Fartousi ya bayyana cewa Hezbollah tana da karfin soji da makamai da suka isa tunkarar Isra'ila.
0 Comments