Sabon Ministan Harkokin Wajen Iran Ali Bagheri Kani Ya Kai Ziyara Lebanon Da Syria Ya Gana Da Ƴan Muqawama.




Daga - Mahadi Tukur Almizan

A karon farko tun bayan shiga Office sabon ministan harkokin wajen kasar Iran mai rikon kwarya ya kai ziyarar aiki ƙasar Lebanon da Syria.

Bagheri Kani ya isa Beirut babban birnin ƙasar Lebanon a ranar Litinin 3 ga watan June da muke ciki, kuma wannan shine karon farko da ya fita daga Iran domin ziyarar aiki tun bayan da ya gaji marigayi Hossein Amir Abdollahian ɗaya daga cikin wadanda jirgin shugaban kasar Iran ya faɗo tare da su a watan da ya gabata.


Tun kafin ziyarar kafar yaɗa labarai ta kasar Iran IRNA ta bayyana cewa ministan harkokin wajen zai kai ziyarar Lebanon da Syria domin tattaunawa da jami'an gwamnatocin kasashen da kuma ƴan muƙawama domin tattaunawa akan yadda za a kawo karshen Isra'ila.



A lokacin da suke ganawa da manema labarai takwaran Bagheri na Lebanon wato ministan harkokin wajen Lebanon Abdullah Bou Habib ya bayyana cewa "Mun yarda cewa dole ne dukkanin ƙasashen wannan yankin musamman ma kasashen Musulmi su yi wata haɗaka domin kawo karshen ta'addancin Isra'ila da kare al'ummar Palestinu musamman a Rafah" ya kuma kara da cewa Muqawama ce kadai zata samar da zaman lafiya a yankin na Gabas ta Tsakiya.



A karshe Bagheri ya mika godiya ga Lebanon bisa nuna alhini da suka yi a lokacin da jirgin shugaba Ra'isi ya faɗi a ranar 19 ga watan May.

Hakanan kuma Bagheri ya gana da Shugaban ƙungiyar Hezbollah Sayyid Hassan Nasrallah tare da rakiyar abokan tafiyarsa da jakadan Iran a Lebanon, a lokacin ganawar Sayyid Nasrallah ya fara da miƙa ta'aziyyarsa bisa rashin shugaba Ra'isi da marigayi Hossein Amir Abdollahian da abokan tafiyarsu.


Sun tattauna dangane cigaban da ake samu kan harkokin tsaro da siyasa a yankin musamman a Gaza da kuma kudancin Lebanon da Hezbollah ke fafatawa da Isra'ila da kuma matakan da ya kamata a dauka domin cigaba da samun nasara.

Daga karshe Sayyid Nasrallah ya mika godiya ga gwamnatin kasar Iran, Jagora Sayyid Qa'id da al'ummar Iran bisa goyon bayan da suke baiwa ƴan Muqawama a faɗin yankin duk da takunkumai da take fama da su.

Hakanan a kasar Syria Bagheri ya gana da shugaban kasar Bashar Al-Asad ba birnin Damascus sun tattauna akan kyautata alaƙar kasashen biyu da kuma cigaban da ake samu a iyakokin Palestinu a ƙwamin da ake.



Shugaba Al-Asad yayi bayanai na karfafawa gamida jinjinawa ga ƴan Muqawama.

Post a Comment

0 Comments