Daga - Mahadi Tukur Almizan
Shugaban ƙungiyar Hamas Yahya Sinwar ya jaddada ma masu shiga tsakani a zaman tattaunawa tsakanin Hamas da Isra'ila cewa Hamas ba zata yarda da wani sharaɗi da yawuce Isra'ila ta dakatar da yaƙi ba Permanently.
Sinwar ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya aika ma kasashen Larabawa da ke shiga tsakani, a cikin sakon na shi ya kara da cewa "Ƴan gwagwarmaya ba za su sallama makaman su ba, kuma za su karbi yarjejeniyar tsagaita wuta ne da sharaɗin dakatar da yaƙin dakatarwa ta din dindin kamar yadda kafar yaɗa labarai ta 'Wall Street Journal' ta wallafa.
"Hamas ba zata sallama makaman ta ba dan haka karka wani ya sake ya nemi hakan" cewar Sinwar ga masu shiga tsakanin.
Sakon na Sinwar ya zo ne a daidai lokacin da shugaban hukumar leken asiri ta Amurka CIA William Burns ya koma Doha babban birnin Qatar domin cigaba da tattaunawa.
Wannan sabon yunƙurin na cigaba da tattaunawar ya biyo bayan kiran da shugaban Amurka Joe Biden yayi na a tsagaita wuta a cikin makon da ya gabata.
Sai dai a ranar Litinin ɗin da ta gabata shugaban haramtacciyar kasar Isra'ila Benjemin Netanyahu ya tabbatar da cewa Isra'ila ba zata yarda da tsagaita wuta na din din din ba har sai ta ga bayan Hamas, Netanyahu ya bayyana cewa za a tsagaita wuta ne domin mu dawo da kamammun mu dake hannun Hamas daga baya sai a cigaba da tattaunawa.
Isra'ila dai tayi watsi da tsarin tsagaita wutar da Amurka ta tsara a baya.
Koda yake a cikin wancan tsarin na Amurka ba a saka dakatar da yaƙin na din din din ba, sai dai Amurka ta nemi a tsagaita wuta na tsawon kwanaki 42, sai a cigaba da tattaunawa bayan an dakatar da hare haren soji daga kowane bangare kamar yadda kafar yada labarai ta Midle Easy Eye ta tabbatar.
Sai dai rashin shigar da babbar bukatar Hamas na cewa a dakatar da yaƙi gaba ɗaya yasa wancan kudurin baiyiwu ba.
0 Comments