Sojojin Isra'ila 70,000 Sun Zama Nakasassu Tabbaci Daga Ma'aikatar Yaƙi Ta Isra'ila.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Ma'aikatar yaƙi ta Isra'ila "Israel War Ministry" ta tabbatar da adadin sojojin da suka samu nakasa a yaƙin Gaza ya haura soji dubu 70, sun kara da cewa akwai ma wasu sojojin guda 8663 da suka samu raunuka tun daga fara yaƙin zuwa yau.

Hakanan kuma a rahoton cibiyar dake kula da masu ciwon ƙwaƙwalwa ta bayyana cewa kaso 35% na waɗannan masu raunukan suna fama da taɓin hankali, sai kuma kaso 21% sune masu raunukan zahiri.

Sashen yana tsammanin samun ƙarin masu raunukan da zai iya cika adadin yakai 20,000 nan da karshen wannan shekara ta 2024.

Masana na hasashen kaso 40% na mutanen da za a kwantar a asibiti daganan  zuwa karshen shekarar nan duk zasu fuskanci matsaloli masu alaƙa da ƙwaƙwalwa, irin ciwon damuwa, tsoro da makamantansu.

Cibiyar "Israel Medical Association" ta fitar da rahoton cewa sababbin marasa lafiya sama da  1,000 suke karɓa a cibiyar su a kowane wata, kaso 20% daga ciki suna fuskantar matsaloli masu alaƙa da ƙwaƙwalwa.

Ko a ranar 7 ga watan da muke ciki na june wani sojin Isra'ila mai suna Eliran Mizrahi ya kashe kanshi bayan an dawo dashi daga fagen fama ya samu cutar taɓin hankali da kuma raunuka har biyu.

Hakanan suma farar hula na Isra'ila masana sun bayyana cewa sama da mutum 500,000 suna fuskantar cutar damuwa da razani ta "Post Traumatic Stress Disorder" (PTSD).

Post a Comment

0 Comments