Ranar 27/06/1981, makiyan juyin Musulunci da ya yi nasara a Iran, suka yi yunkurin hallaka jagoran juyin Musulunci a Iran na yanzu, Ayatullahi Sayyid Ali Khamenei, lokacin da yake gabatar da huduba a Masallacin Abu Zar.
Yana cikin gabatar da huduba, kawai sai radiyon daukar sauti na kaset, wadda aka ajiye tana kallon inda yake, da Sunan daukar hudubar, ta tarwatse, abunda ya yi sanadin jikkatarsa, a hannayensa 2, wasu jijiyoyin hannun damansa suka tsittsinke, abuna ya yi sanadin shanyewar hannun baki daya.
Ga fassarar wasikar jaje da Imam Khumaini ya aike masa lokacin yana jinya.
"Da Sunan Allah mai yawan Rahama mai yawan Jinkai.
Mai girma Hujjatul Islam Hajj Sayyid Ali Khamenei Allah ya wanzar da kwararar albarkarsa.
Ina godewa Allah mai girma da daukaka, da ya mayar da makiyan Musulunci wawaye, kamar yadda kuma nake gode masa, da ya sa tun farkon juyin Musulunci mai girma, duk sadda suka kitsa da shirya makirci, suka yi fade-fade, hakan na kara dunkule al'ummarmu mai sadaukarwa wuri guda ne, tare da kara damfarewa juna. Wannan ya ke kara gaskata riwayar da ke cewa: "Addinin nan ba zai gushe ba yana Dada samun karfi da mutane fajirai".
Hakika sun yi yunkurin hallaka Wanda sautin Addu'ar sa yake raurawa a kunnuwan musulmin duniya. Da wannan danyen aikin basu, maimakon cusa tsoro a zukatan muminai, sun ma kara himma ne da dakewa ga miliyoyin musulmi, sun sake daidaita sahunsu fiye da baya.
Ashe har yanzu lokaci bai yi ba, bayan duk wadannan miyagun aiyukan laifi na dabbanci na wadannan mutane, da matasan da aka yaudara zasu fice daga tawagar wadannan maciya amana?
Ashe lokaci bai yi ba, da iyaye maza da mata zasu taka birki daga sallama matasan ya yansu masu girma ga wadannan mabarnatan ba? Su kuma gargade su daga tsoma hannu a irin wadannan miyagun aiyuka ba?
Shi ko sun san cewa suna bata lokacin samartakarsu a banza da wofi, ta hanyar yin irin wadannan miyagun aiyukan, suna sallama rayuwarsu, Dan biyan bukatun kashin kai ne, na gungun wasu lalatattun mutane?
Mu kam, ya isa abun alfahari gare mu a gaban Allah da waliyyin Allah, wanzajjen Allah -rayukanamu fansa gare shi- da wadannan dakaru na fagen daga, da na bayanta, wadanda suke rayar da dararensu da ibadodi, su kuma raya yinnansu cikin jahadi a tafarkin Gaskiya.
Hakika Ni, ina alfahari da kai ya Khamenei mai daraja, ina taya ka murnar hidimarka a fagen daga da kakin soja, da hidimarka a bayan fagen daga da tufafin malamai, a matsayin mai hidima ga wannan al'umma da aka zalinta.
Ina roko, daga Allah madaukaki, ya ba ka lafiya Dan ka cigaba da hidima ga Musulunci da musulmi.
Amincin Allah da rahamarsa da albarkokinsa su tabbata gareku.
Ruhullah al-Musawi al-Khumainiy".
Fassarata: Nasir Buba Azam
27/06/2024
0 Comments