Daga - Yusuf Kabir
A na masa lakabi da "Shahidi mai rai" saboda ya sami raunuka a sad da yana aikin Soji na dakarun juyin Musulunci na Iran IRGC a yakin Irak-Iran.Shi kwararren Lakcara ne a Jami'ar Imam Sadiq (as) a Yayin da yake karantar da "Diplomasiyyar daga Annabi da iyalansa" ya kware a yarukan Turanci da Larabci da Kuma Farisanci Yana cikin mutane 500 masu tasiri a Duniya.
Jalili mai ra'ayin rikau ne ma'ana Yana da ra'ayi irin na Gen.Sulaimani, Shaheed Ra'esiy,Fakar Zadeh,Hasan Shadariy da sauran dakarun juyin Musulunci.Sayyid Mujtaba Khamne'i ya siffanta Jalili da cewa:"Mutum ne mai Imani da sallamawa da son ci gaban tsare-tsaren Nuclear din Iran,Sannan ba ya da sassauci.
kabiruyusuf533@gmail
Shi ma mai fashin baƙi kan al'amuran siyasar duniya Dr. Shamsuddeen Hassan yayi tsokaci akan Saed Jalili
"Dr. Saeed Jalili Filosofah ne Mufakkir mai school of thought Mai zaman kanta a ƙarƙashin Nizamin Musulunci. Ƙashin bayan Fikirarsa ya debosu ne daga Khomeinanci."
"Islamic scholar ne mai yin bahasoshi masu zurfi dangane da Tafsir, Siyasar Musulunci, Akhlaq, da Saqafah".
Dr. Shamsuddeen ya ƙara da cewa "Jalili yana da bahasoshi masu faɗi a cikin Nahjul Balagha, Falsafar Musulunci da Tarihi. Sannan gashi Gwararren Muballigi, cikakken Orator. Abunda ya fi burgeni dashi shine kokarin aikata abunda yayi imani dashi, Gwargwadon iko, bisa Nizami irinna Institutions da foundations, shigen irin na Jagoran Harka Islamiyyah a Najeriya".
"Jalili yana da himma irinta Ra'isi, ga shiga rai irin na Sulaimani".
"Ya iya karri, ya iya farri. Komai nasa tsaf, komai nasa cif. Cif, cicif cif".
Dr. Shamsuddeen ya bayyana cewa "Duk cikin 'yan takarar kowa nada babbar manufar ciyarda Iran gaba, kuma da gaske suke. Hatta zafi ga Magauta akwai irinsa a cikinsu wato Qalibaf. Abu ɗaya ne Jalili ya fi sauran a wajena shine;
"Shi Kaɗai ne a cikinsu yake niyyar canja foreign policy dinda aka San Iran da fiye da shekaru 1000. Jalili yace zai sauya policy na "strategic patience" wanda aka san Iran dashi, har ya zamo tamkar wani ɓarayi na Jikinta, zuwa policy dinda "Wa'adus - Sadiq" ya kawo".
"Wa'adus Sadiq shine sunan Harin da Aminin Ra'isi Aminin Jalili ya kaiwa Isra'ila kowa na gani, inda ya zaneta a gaban Walidai".
Wannan kuma ɗaya daga cikin mafarkin juyin musulunci na Iran ne. Idan Jalili ya ci zai yi hulɗa da kasashen Duniya ne a kan Qa'idar
و كلت للخل كما كال لي على و فاء الكيل أو بخسه.
0 Comments