WANENE DR.MAS'UD PEZESHKIAN? WANDA YAKE KAN GABA DA KURI'U (10,415,991) ZABEN IRAN?)

 


Daga Yusuf Kabir.


Sunansa Dr.Mas'ud Pezeshkian an haife shi a September shekarar 1954 a garin Mahbad.Mahaifinsa Dan garin Azarbiajan ne na Iran,sannan Mahaifiyarsa 'yar Ba'iraniya ce Bakurdiyya


Ya fara siyasa ne a sad da ya shiga cikin gwamnatin tsohon Shugaban Qasa Muhammad Khatami mai sassaucin ra'ayi.A Yayin da ya rike mataimakin Ministan lafiya a 1997,Sannan ya yi Ministan lafiyar Iran  a tsakanin  2001-2005.


Ya fara takarar Shugaban in kasa a 2013 sai dai ya janye daga baya,Sannan an ba shi tikitin  takara a 2021 sai dai ya ki karba.


Pezeshkian  ya kasance Wanda aka san shi da karfafar dakarun juyin Iran IRGC,Sannan Malamin Alkur'ani ne wanda yake yawan nazarin littafi Nahjil Balaga.


Pezeshkian ya sokin tsarin juyin Musulunci saboda mutuwar Mahsa Amini a 2022 sakamakon hukunta ta da dakarun juyin Musulunci suka yi.



Post a Comment

0 Comments