Yadda Yaƙin Gaza Ya Rusa Project Ɗin Amurka Mai Suna 'IMECs'

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Ƴan gwagwarmaya ba kawai Isra'ila suka gasa ma aya a hannu ba har Amurka sun rusa ma manyan Geopolitical Projects ɗin ta na Yammacin Asia ciki har da IMEC's ( India-Middle East - Europe Economic Corridor, domin kuwa wannan Project ɗin an tsara shi ta yadda Isra'ila ta kasance jigo a ciki domin itace babbar mahaɗar wannan project ɗin da zai haɗa Gabashin Duniya da Yammacin Duniya.

Kasantuwar A Yanzu Amurka na gasa da China in Economic Field shiyasa take ƙoƙarin kishiyantar Project ɗin China mai suna Belt and Road Initiative (BRI)

Abubuwan da suka dagula wannan project na Amurka sun hada da hare haren da Hezbollah ke kai mata tun daga ranar 08 October na shekarar 2023 zuwa 5 March 2024 Hezbollah takai adadin hare hare 1,194.

A gefe guda kuma ga Yemenawa wanda suka kaddamar da hare haren da suka dagula duk wata harkar Jiragen dakon kaya da tashoshin su, musamman tashoshin kudancin Isra'ila.

Domin a cikin watan December na shekarar 2023 Shugaban tashar jiragen ruwa ta Eilat ya bayyana ma kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ayyukan tashar jiragen ruwan ta Eilat sun sauka da kaso 85 sakamakon hare haren Yemenawa a Red Sea, wannan fa tun a watan December kenan.

Sannan wannan yaƙin ya durƙusar da tashar jirage ta Ashkelon da matatar man Isra'ila ta Ashkelon ɗin wadda itace mafi kusa da zirin Gaza, tashar Ashdod tana da nisan kilomita 40 daga arewacin Gaza a gabar Bahar-Rum (Mediterranean Sea) babban daraktan rikon kwarya na tashar Eli Bar-Yosef a makonni biyu na bayan harin 7 October, ya bayyana cewa Isra'ila ta shiga matsin da ya takurata ta kwashe Kwantinoni (Containers) guda dubu 11 daga tashar Ashdod zuwa wasu tashoshi dake arewacin kasar, har tashar Haifa itama ta fuskanci hare hare daga ƴan gwagwarmaya na Iraqi wannan ya rusa yardar ko natsuwar da kamfanoni suke da ita da  Isra'ila kasancewar wannan tashar wata madogara domin itace mahaɗa tsakanin Asia da Turai.


A ranar 27 ga watan April kuma wata sabuwar ƙungiyar ƴan gwagwarmaya ta shiga sahun masu kaima Isra'ila hari, wannan ƙungiya kuwa itace 'Saraya Al-ashtar' wato Al-ashtar Brigade daga Bahrain inda suka hari bangaren kamfanin Isra'ila mai suna 'Trucknet' dake Eilat, wanda wannan kamfanin yana da alaka da wancan project ɗin na Amurka IMEC's, wannan kuma shine ya ƙara jefa kokwanton yiwuwar wannan project ɗin na Amurka.

A watan September na shekarar da ta gabata ne shugaban kasar Amurka Joe Biden ya sanar da wannan project na IMEC's a taron G20, inda ya bayyana kasashen da za su yi musharaka a wannan project wanda suka haɗa da India, Saudi Arabia, Dubai daga Asia saikuma Isra'ila, Faransa, Germany, Italy, da kuma Amurka daga Turai.

Fadar gwamnatin Amurka ta bayyana cewa wannan project ɗin zai karfafa harkokin kasuwanci inda zai samar da titin jirgin kasa, bututun Hydrogen da wasu abubuwa na kasuwanci wanda zai haɗa Asia da Turai, sannan titin jirgi da bututun Hydrogen zasu taso daga India su shiga ta Dubai, su ɓulla ta Saudi Arabia su shiga ta Jordan su shiga Isra'ila daganan su tsaya a tashar Piraeus dake Girka (Greece).

Tun bayan wannan sanarwa Amurka ke ta faɗi tashin ganin nasarar wannan project.

Sai dai a yanzu ana iya cewa yiwuwar wannan project ɗin ya ta'allaka da samun zaman lafiya a yankin, muddin babu zaman lafiya to wannan project ɗin bazai yiwu ba kasantuwar bangarorin gwagwarmaya suna iya kaima Isra'ila hari ta kowace fuska.

Ga shi kuma a kwanan nan Yemenawa sun sanar da faɗaɗa hare haren su zuwa Bahar-Rum (Mediterranean Sea).

Hakanan kuma wannan yaƙin ya rusa kokarin da Amurka take yi na daidaita tsakanin Isra'ila da Saudi Arabia kafin ɓarkewar yaƙin gashi kuma kasashen biyu na daga cikin ginshiƙan wannan Project ɗin.



Abinda ya ƙara jefa wannan project cikin tsaka mai wuya a halin yanzu shine Isra'ila ta ƙi amincewa da sharuɗɗan da Saudi Arabia ta gindiya mata Indai har za su daidaita tsakanin su, wannan sharaɗin kuwa shine dole Isra'ila ta amince a  baiwa Palasɗinawa ƙasar su wato ayi "Two State Solution" Palasɗinawa su zamo kasa mai zaman kanta suma Isra'ila haka, sai dai Netanyahu ya ƙi amincewa da hakan.


Saudi Arabia kuma ta ja tunga tace lallai wannan ne kaɗai lafiyar da zata samar da daidaito a tsakanin su.

Post a Comment

0 Comments