Yemenawa Sun Mayar Da Martanin Harin Da Amurka Da Ingila Suka kai Masu: Sun Hari Jirgin Ruwa Mai Ɗaukar Jiragen Sama Na Yaƙi "Eisenhower".

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Amurka da Ingila sun kai hari Yemen wanda yayi sanadiyyar shahadar mutum 16 kuma ya jikkata mutane da yawa a babban birnin ƙasar da kuma wasu yankuna a ranar 30 ga watan May da ya fita.

Su kuma rundunar sojin Yemen sun fitar da sanarwar harin mayar da martanin da suka kai kan jirgin Amurka USS Eisenhower dake ɗaukar jiragen sama na yaƙi a Read Sea a ranar 31 ga watan May ɗin.

Brigadier General Yahya Saree ne ya sanar da wannan hari inda ya bayyana cewa " A mayarda martanin barnar Amurka da Ingila, bangaren sojin saman Yemen sun yi haɗaka da sauran bangarorin sojin wajen harar jirgin dakon jiragen sama na yaƙi mallakin Amurka a Red Sea, anyi amfani da ballistics missiles wajen kai wannan hari kuma anyi nasarar samun hadafi" a cewar Yahya Saree.

Ya kara da cewa "Dakarun sojin Yemen ba za su yi ƙasa a gwuiwa ba wajen mayar da martani kaitsaye kuma da gaggawa a duk lokacin da aka hari iyakar ƙasar". 

Amurka ta girke wannan jirgin na Eisenhower ne tun ranar 13 ga watan October kwanaki kaɗan bayan kaddamar da Ɗuufanul Aqsa.

Sai dai jirgin ya bar Red Sea a cikin watan April sannan kuma ya sake dawowa cikin watan May.

A cikin bayanin Yahya Saree ya bayyana cewa tun daga lokacin da Amurka da Ingila suka fara kai hare hare Yemen sun kashe mutum 58 tsakanin soji da farar hula.



A wannan harin da suka kai ranar 30 ga watan May ɗin sun kashe mutum 16 kuma sun raunata mutum 41, sannan sun lalata abubuwan more rayuwa na al'ummar Yemen.

Wannan harin na Amurka ya zo ne bayan kwana biyu da dakarun sojin na Yemen suka harbo jirgin Amurka "US MQ-9" wanda darajar shi ta kai dalar Amurka miliyan 30 ($30Million), wanda ya zamanto karo na 6 suna kama irin wannan jirgin tun daga watan November.

Gwamnatin kasar Yemen tana kara tabbatar da cewa ba za ta daina harar Jiragen Isra'ila da masu alaƙa da ita ba har sai sun dakatar da duk hare haren su kan al'ummar Palestinu.

Post a Comment

0 Comments