A ƴan kwanakin nan a Garin Parachinar garin da ke da kaso 95.5 cikin ɗari(95.5%) mabiya Mazhabin AhlulBayt(AS) ƴan [Shi'a] ma zauna garin na fuskantar hare-haren kungiyoyin ta'addanci wanda suke haɗin gwiwa tsakanin Wahabiyawan Fakistan da Afghanistan masu tsatsauran ra'ayi, rayuwar raunanan bayin Allahn a wanan yankin ya zama ko in kula inda har ƴan ta'adda sukan rufe garin dukka ta ɓangarori 4 ba shiga ba fita.
Suna ci gaba da kashe ƴan Shi'a, inda suka ɗauki ransu agunsu ba kome bane inda har a kafafen yaɗa labarai da sadarwa ba'a yaɗa labarin abinda ke faruwa, kuma Gomnati da Sojojin Fakistan sunyi shiru basu kai musu ɗauki ko taimakon gaggawa ba, suna kallo ana kisan kiyashi kan #Yara, Mata, Dattijai da matasa.
A shekaran Jiya Juma'a da Asabat ne haɗin gwiwar ƴan ta'addan Wahabiyyawah masu Iƙrarin Jahadi daga Fakistan da ƙasar Afghanistan(Ta*li*ban) suke kai mummunan hari kan musulmi mabiya Mazhabin AhlulBayt(AS) [Shi'a) dake zaune a garin na #Parachinar inda sukayi kisan kiyashi tare da anfani da Bama-bamaj da bindigogi akan raunana ƴan Shi'an kamar yanda Haramtacciyar ƙasa keyi wa Raunanan Al'ummar Falasɗinu.
A sakamakon harin ne yayi Shahadar kimanin mutane sama da 25 cikinsu da yara ƙanana, inda sama da 100 suka jikkata, a wannan shekarar na 2024 ba shine karo na farko wajen kaiwa irin wanan harin ba.
Kamar yanda HKI ke ci gaba da kai hare-haren kan raunanan Falasɗinu a Gaza Haka waɗannan kungiyoyin ta'addancin ke kisan ƴan Shi'a a wanan yankin baya ga tada musu Bama-bamai a wajajen taronsu su kashe na kashewa su harbe na harbewa kuma Gomnati da gidajen jaridu da kafafen watsa labarai suyi jugum ana kisan kiyashi.
Halin da ake ciki yanzun haka a #Parachinar na ƙara ta'azzara, adadin wadanda ake kashewa na karuwa, asibitoci cike suke da waɗanda aka raunata gashi ba isassun magani da wuraren da za'a ajiye marasa lafiya.
Idan zamu ci gaba da ɗaga murya kuma muka damu dangane da al'amarin Falasɗinu, amma kan al'amarin #Parachinar mukayi shiru shima Allah zai tambaye mu, kuma a munafukai zamu tashi.
Magana Ake na ƴan Adamtaka, Kare rai daga Mashaya jini da nuna goyon baya ga raunana da taimakonsu da abinda zamu iya ayi.
Oppecial Taekwond Al'ameen
Activist • Freedom Fighter • Resistant
23th Muharram, 1446,
29th July, 2024.
#StopShiaGenocide #StopKillingPalestine #ParachinarUnderAttack #ShiaLivesMatter #PrayForPalestine #FreeThemAll #JusticeForAll
0 Comments