Daga naku - Muhammad Attahiru🎙️
Gwamnatin Jamus ta bayar da umarnin rufe cibiyar Muslunci ta Hamburg da sauran cibiyoyin da ke da alaƙa da ita a fadin ƙasar, bisa zargin yaɗa tsatsauran ra'ayi da aƙidar Musulunci mai tsaurin ra'ayi.
Da sanyin safiyar Laraban da ta gabata ne ƴan sanda su ka kai samame a wasu kadarori 53 da ke da alaka da IZH a cikin jihohi takwas na Jamus. Hare-haren sun yi sanadiyar kwace wasu kadarori tare da rufe masallatai hudu. Har ila yau, haramcin ya shafi cibiyar IZH a Frankfurt, Munich, da Berlin.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranan Laraba, ministar harkokin cikin gidan Jamus Nancy Faeser ta sanar da dakatar da cibiyar Islama ta Hamburg (IZH) saboda biyar manufar kishin Islama.
Ta bayyana cewa ƴan sanda na gudanar da bincike a shahararren ‘Blue Mosque’ da ke ƙarƙashin cibiyar IZH. Faeser ta kara da cewa "Cibiyar Musulunci ta Hamburg da kungiyoyin da ke da alaƙa da ita suna yiwa kasar Jamus zagon ƙasa ta hanyar inganta aƙidar Islama da tsattsauran ra'ayi da ke adawa da mutuncin bil'adama, ƴancin mata, tsarin shari'a mai zaman kansa, da gudanar da mulkin dimokradiyya."
Ana zargin kungiyar IZH da ke gudanar da masallacin Imam Ali (wanda aka fi sani da Blue Mosque) - daya daga cikin tsofaffin masallatai a ƙasar Jamus - da goyon bayan kungiyar Hizbullah ta Lebanon wacce ta shahara wajen daƙile ci gaban sojojin Isra'ila a Labanon a shekarun 2000 da 2006 da Jamus ta ayyana a matsayin kungiyar ta'addanci a shekarar 2020.
A wani samame makamancin haka a watan Nuwamban da ya gabata, hukumomin Jamus su ka kai samame kan wasu kadarori 55 da ke da alaƙa da kungiyar. Ƴan sanda sun kama wasu kaya da ake zargin IZH na gudanar da ayyukanta ne a hankali cikin tsauri tare da ƙoƙarin ɓoye manufofinta na siyasa, duk da cewa ma’aikatar ba ta fayyace irin shaidar da aka tattara ba.
Cibiyar Musulunci ta Hamburg ta ci gaba da yin Allah wadai da duk wani nau'i na tashin hankali da tsattsauran ra'ayi, tare da bayar da shawarar samar da zaman lafiya, hakuri, da tattaunawa tsakanin addinai. Masallacin IZH da 'Blue Mosque' da ke kan Alster, wanda IZH ke tafiyar da shi, na amfani da shi ne a matsayin cibiyar tuntuba ta mabiya mazhabar Shi'a na ƙasashe daban-daban.
Ana raya addu'o'i na yau da kullun da kuma bukukuwan Addini. Bugu da ƙari, ana gudanar da ayyukan koyarwa iri-iri a wurin - alal misali, koyarwar Addinin Musulunci ga yara da kuma koyar da harsunan Larabci, Farisa, da Jamusanci.
Wata majiya da ke kusa da Cibiyar Musulunci a Jamus da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana harin da ƴan sandan suka kai a baya-bayan nan a matsayin tashin hankalin da ba a taba ganin irinsa ba a wata hira da kamfanin dillancin labaran Iran IRNA.
Majiyar ta bayyana cewa, a lokaci guda jami'an ƴan sanda sun kai farmaki kan cibiyoyin Addinin Musulunci a Frankfurt, Berlin, Munich, da Hamburg da safiyar ta Laraba, inda suka kwace kadarori da dama.
Majiyar ta ruwaito cewa, ƴan sanda sun shiga harabar Masallacin da karnuka, inda suka yi watsi da harkokin Addini, kuma sun shafe sa’o’i da dama suna gudanar da bincike. Bugu da kari, gidajen jami'ai, daraktoci, limamai, da ma'aikatan wadannan cibiyoyi na kewaye ne da ƴan sandan Jamus, lamarin da ya sa ba a iya tuntubarsu.
Har wala yau majiyar da aka sanar ta kuma bayyana wannan farmakin a matsayin wani hari mai tsanani da gwamnatin Jamus ta kai kan cibiyar Addini wanda ba a taɓa ganin irinsa ba.
Majiyar ta kuma yi watsi da zargin da hukumomin Jamus ke yi na alaƙa tsakanin cibiyoyin Musulunci guda hudu da ke Hamburg, Berlin, Munich, da Frankfurt, ko kuma da wata gwamnati. Sun kuma jaddada cewa wadannan cibiyoyi suna gudanar da ayyukansu ne bisa ƙashin kansu, kuma tarihinsu ya samo asali ne tun kafin juyayin juya halin Musulunci ta Iran.
Majiyar ta ci gaba da cewa, ayyukan wadannan cibiyoyi sun cika ka'idoji da dokokin Jamus. Al’umma ce ke tantance limamai, daukar ma’aikata, kuma hukumomin Addini ne suka amince da su, kuma suna tallafa musu.
Har wala yau, majiyar ta bayyana ayyukan cibiyoyin na Musulunci a nan Jamus a matsayin cibiyoyi masu gudanar da ayyuka kamar: bukukuwan Addini, samar da zaman lafiya, abokantaka da zaman lafiya, tare da jaddada cewa waɗannan cibiyoyin ba su aiwatar da wani mataki da zai kawo cikas ga tsaron kasar ta Jamus ba.
Wani kwamiti mai zaman kansa da gwamnatin Jamus ta kafa a bara ya ba da rahoton cewa a kullum Musulmi a Jamus na fuskantar wariyar launin fata, ƙiyayya da wariya. Rahoton ya yi nuni da cewa, a kullum Musulmi a Jamus na fuskantar kyama da nuna wariyar launin fata.
Matakan da gwamnati ta ɗauka kan cibiyoyin Musulunci a Jamus a halin yanzu ya haifar da damuwa game da ƴancin Addini da yadda ake mu'amala da al'ummar Musulmi a kasar.
Bayan dakatarwar, babban kamfanin dillancin labaran kasar Turkiyya AA, ya bayar da rahoton cewa, hukumar kula da harkokin Addini ta kasar Turkiyya ta bayyana damuwarta a kan haramcin da aka sanya wa cibiyar Islama ta Hamburg, inda ta bayyana cewa wannan mataki ne na rashin adalci a kan Musulmin da ke zaune a Jamus.
Ku ci gaba da kasancewa da wannan shafi na Freedom Fighters Ng mai ɗauke da ingantattun bayanai masu ilmantarwa dangane da irin abubuwan da ke faruwa a faɗin duniya.
0 Comments