Daga - Mahadi Tukur Almizan & Abdurrahman Bala Idris
Hezbollah ta sanar da kai jerin hare-hare a ranar Juma’a, inda ta kai hari kan wuraren da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka mamaye a arewacin kasar Lebanon.
Hezbollah ta kuma gabatar da makami mai suna Wabel IRAM (Improvised rocket assisted munition), sun yi amfani da shi wajen kai hari kan sansanin sojojin Isra'ila kusa da kan iyakar Lebanon da Falasdinu.
Biyo bayan kashe fararen hula da Isra'ila ke ci gaba da yi a kudancin kasar Labanon, a ranar Larabar da ta gabata Sayyid Hasan Nasrallah ya sanar a ranar Laraba cewa, duk wani hari da aka kai kan fararen hula, kungiyar Hizbullah za ta kai hari kan sabbin matsugunan Isra'ila da ba a kai wa hari ba.
Kwana guda bayan alƙawarin Sayyed Nasrallah, 'yan mamaya sun yi ruwan bama-bamai a ƙauyuka uku a kudancin Lebanon:
Safad al-Batikh
Majdal Selm
da Shaqra.
Wanda ya yi sanadiyar shahadar fararen hula fiye da goma.
Sai dai dakarun Hezbollah sun mayar da martanin wannan hari, inda suka sanar cewa sun harba rokoki da ake kira 'Katyusha Rockets' zuwa matsugannan ƴan mamaya dake Abirim settlement a arewacin Palasɗinu, wannan shine karon farko da suka Kaima wajen hari.
Da misalin karfe 9:30 na safe ne mayakan Hezbollah suka kai hari a sansanin sojin Ruweisat al-Qarn da ke gonakin Shebaa na kasar Lebanon da suka mamaye tare da yin amfani da roka mai nauyi ƙirar cikin gida da ake kira Wabel IRAM, wannan makami yayi nasara domin ya samu inda aka so, ya yi ɓarna kuma ya tayarda wuta a wurin.
Har ila yau mayakan na Hezbollah sun kai hari kan sojojin Isra'ila da ke kusa da barikin Raim da makamin roka na Burkan da kuma wurin Metula da makaman atilari da tsakar rana, kuma makamin sun samu duka wajen biyu.
Da misalin karfe 12:13 na dare, mayakan na Hezbollah sun sake kai hari a wuraren da sojojin Isra'ila suka tare a Khirbet Ma'ar da kuma sojojin Isra'ila da ke kusa da wasu manyan rokoki na Katyusha da Falaq, inda suka kai musu hari kai tsaye.
A wasu hare-hare guda biyu na mayar da martani ga asarar rayukan fararen hula a yankunan Safad al-Batikh, Majdal Selm, da Shaqra, Hezbullah ta sanar da kai farmaki kan matsugunan Neveh Ziv da Manot a karon farko da makamin Katyusha, bayan harin Abirim.
Har ila yau kungiyar ta Hezbollah ta sanar a ranar asabar cewa ta kai hari kan gine-ginen da sojojin Isra'ila ke amfani da su a matsugunin al-Manara da makaman da suka dace, inda suka kai hari kai tsaye.
Kungiyar Hizbullah ta sanar da kai hare-hare kan sansanin soji na al-Marj da makaman artillery da karfe 4:10 na yamma, inda ta tabbatar da kai hare-hare kai tsaye.
Ta hanyar amfani da jirgi mara matuki, Hezbollah ta ce ta kai hari tare da lalata kayan aikin fasaha da aka sanya a Al-Abad.
Da misalin karfe 5:23 na yamma, kungiyar Hezbullah ta sanar da kai hari a karo na biyu a biya, inda ta kai hari a rukunin Ruweisat al-Qarn da ke gonakin Shebaa na kasar Labanon da makaman roka. Hezbollah ta tabbatar da samun inda ta harba.
A gefe guda kuma, kungiyar ta Hezbollah ta ce mayakanta sun kai hari ne da misalin karfe 6:00 na yamma a wurin al-Samaqa da ke tsaunin Kfar Chouba da suka mamaye da makaman roka.
A wani samame mai inganci, dakarun Hezbullah sun kai hari kan wuraren da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suke a arewacin matsugunin Ein Yaakov da ke arewacin Palasdinu da ta mamaye.
Daga nan ne aka kai hari a sansanin sojin Isra'ila na al-Malikiya da makaman artillery da karfe 6:50 na yamma, inda aka kai musu hari kai tsaye.
Dangane da harin da Isra'ila ta kai kan Safad al-Batikh, kungiyar Hezbollah ta sanar da gudanar da ayyuka guda biyu.
Harin farko ya nufi barikin Yiftah ne da roka mai linzamimai suna Jihad heavy rocket.
0 Comments