Hizbullah Ta Yi Luguden Wuta Kan Hedkwatar Rundunar Sojin Isra'ila ta 91 Division da ke Ayelet.

 


Daga - Abdurrahman Bala

Hezbollah sun kai hare-hare hudu kan ƴan mamaya  a ranar 14 ga watan Yuli a cigaba da hare haren goyon bayan Falasdinu da kare kudancin Lebanon.



Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Lebanon- Hizbullah ta kai jerin hare-hare a kan iyakar Lebanon da Falasdinu, domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu da  'yan gwagwarmayar 'yantar da Palastinawa, da kuma kare kauyukan kudancin Lebanon dake cigaba da nuna turjiya ga hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da yi. 


A jiya 14 ga watan Yulin da muke ciki kungiyar Hizbullah ta kai hare-hare guda hudu a kan yankin Arewacin Isra'ila, kamar haka:



1. Da karfe 10:45 na safe ne mayakan Islamic Resistance suka kai hari da makami mai linzami a kusa da yankin Hadab Yarin na Isra'ila da makaman rocket.


 2.A matsayin martani ga hare-haren da Isra'ila ta kai kan kauyukan kudancin Lebanon musamman hare-haren da aka kai a garuruwan Arnoun da al-Khardali, mayakan Islamic Resistance sun kai wani samame ta sama tare da tawagar jiragen sama marasa matuka kan sabuwar runduna ta 91 a hedkwatar  bayarda umarni na rundunar dake  Ayelet.


 An kai harin ne a wuraren da jami’anta da sojoji suke, inda aka tabbatar da asarar rayuka. 



3. Da misalin karfe 3:10 na rana, mayakan Islamic Resistance sun kai hari kan inda aka jibge sojojin mamaya na Isra'ila a kusa da Roueissat al-Alam a tsaunin Kfar Chouba na Lebanon da aka mamaye da makamin roka na Burkan. 


4. Da misalin karfe 6:05 na yamma, mayakan na Resistance sun kai hari a yankin al-Ramtha da ke tsaunin Kfar Chouba na kasar Labanon da makami mai linzami inda suka kai farmaki kai tsaye kuma cikin nasara.



 Hezbollah ta fara kaddamar da hari da wani jirgi mara matuki kirar Shahed-101 a ‘Isra’ila.


Hezbollah ta kaddamar da wani jirgin sama mara matuki na Iran Shahed-101 a arangamar da aka yi a kudancin Lebanon, wani jirgin samane mai sarrafa kansa wanda ke da wahalar ganowa, lamarin da ya jefa firgici ga ƴan mamayar.


 "Hizbollah ta fara amfani da sabbin jiragen Shahed 101 na Iran a karon farko tun farkon yakin," in ji Itay Blumenthal, wakilin harkokin soji na ma'aikatar yada labarai na Haramtacciyar ƙasar Isra'ila.


Wadannan jirage marasa matuka "suna da matukar wahala ga Sojan Sama wajen ganowa da kuma iya dakile harinsu."


 Blumenthal ya kara da cewa, wadannan sabbin jirage marasa matuka masu amfani da wutar lantarki ne, sabanin jiragen Ababil da Hezbollah ke amfani da su a baya, wadanda suke amfani da mai. Ya lura cewa "Basu da kara sosai kuma kusan ba za a iya jin ƙarar su daga  ƙasa ba." Ya kara da cewa, "Wadannan jirage marasa matuka suna iya nisan  kilomita 19 kuma suna iya daukar abubuwan fashewa masu nauyin kilo 10." 


Ya tabbatar da cewa, su ne jiragen da kungiyar Hizbullah ta harba a ranar Alhamis, wadanda suka kai ga kashe wani jami’in rundunar Alon Brigade, tare da gano ragowar a kusa da Kibbutz Kabri.

Post a Comment

0 Comments