Isra'ila Ta Aikata Kisan Kiyashi Kan Al'ummar Palasɗinu Sau Uku Cikin Ƙasa Da Awa Ɗaya.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Aƙalla Palasɗinawa 40 ne suka rasa rayukansu a wani ƙazamin hari da Isra'ila ta kai kudanci,tsakiya da arewacin zirin Gaza.


Sojin Isra'ila sun aikata sabon kisan kiyashi kan Palasɗinawa fararen hula a ranar Talata 16 ga watan July.


Ministan lafiya na Gaza ya shaidawa wa manema labarai a jiya Laraba 17 ga wata cewa an kashe aƙalla mutum 17 ciki har da ƙananan Yara sannan wasu mutum 26 sun samu raunuka a harin da Isra'ila ta kai unguwar Al-Attar dake kusa da Al-Mawasi kudancin birnin Khan Yunis.


 

Isra'ila ta yi ikirarin cewa ta hari Kwamandan rundunar 'Palestinian Islamic E (PIJ)' ne.


Hakanan sojin na Isra'ila sun yi ma makarantar hukumar UNRWA dake  sansanin gudun hijira na Nuseirat Camp dake tsakiyar Gaza ƙawanya inda suka kashe aƙalla Palasɗinawa 23 wasu da dama kuma suka jikkata, cikin waɗanda suka yi shahada har da ƙananan Yara, Isra'ila tayi iƙirarin cewa akwai ƴan Hamas da suka fake a makarantar.


Hakanan sojin Isra'ila sun kashe Palasɗinawa 4 a arewacin birnin Beit Lahia sannan sun raunata wasu mutum 5, a harin da suka kai kusa da shataletalen  'Sheikh Zayed Roundabout'.


Kafar yaɗa labarai ta Aljazeera ta bayyana cewa jimullar adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a waɗannan hare haren yakai mutum 40.


A ƴan kwanakin nan dai Isra'ila ta tsananta kisan kiyashi kan al'ummar Palasɗinu.


Ko a ranar 14 ga wata Isra'ila ta kai hari wata  makaranta mai suna Abu Oreiban School dake ƙarƙashin kulawar hukumar UNRWA ta majalisar ɗinkin duniya, inda ta kashe aƙalla Palasɗinawa 15, wasu mutum 70 kuma suka samu raunuka.


Hukumar lafiya ta Palasɗinawa ta bayyana cewa Isra'ila ta kai hare haren kisan kiyashi a makarantun Palasɗinawa sama da sau 40 daga fara yaƙin nan a watan October na shekarar da ta gabata.



Ko a ranar 13 ga wata Isra'ila ta kai hari sansanin gudun hijira na Al-Mawasi inda ta kashe aƙalla Palasɗinawa 90 a harin da ta kai da jiragen sama.


A cikin makon da ya gabata makarantu 4 Isra'ila ta kai ma hari a tsakanin kwana 4.

Post a Comment

0 Comments