Isra'ila Ta Kashe Wani Ɗan Kasuwa Mai Alaƙa Da Ƙungiyoyin gwagwarmaya.

 


Daga - Abdurrahman Bala Idris

Muhammad Al_Katerji babban dan kasuwar da ake zargi da tallafawa mayakan gwagwarmaya kamar Hizbullah, an kasheshi ne a kusa da iyakar Kasar siriya da Lebanon.


Muhammad Barraa Al-katerji dai babban dan kasuwa ne dake da kyakkyawar alaka da mayakan gwagwarmaya kuma an kashehi ne a ranar 15 ga watan Yuli, lokacin da haramatacciyar ƙasar Isra'ila takai farmaki kan iyakar kasar Siriya da Lebanon.


Al-katerji dai yayi shahada ne a garin Saboura a bangaren siriya dake da iyaka da Lebanon a yammacin ranar Litinin da ta gabata.


Barrah Al-katerji dai hamshakin dan kasuwa ne a dukkan yankunan kasar Syria, tareda dan'uwan sa Hussam sun gina harkokin kasuwanci da yawa da suka hada da sana'ar mai, gine gine, tsara birane, da kuma harkokin sufuri, dukkansu biyun sunada kusanci da shuganan kasar syria Bashar Al-assad.


Haramtacciyar ƙasar Isra'ila na zarginsa da hannu dumu-dumu cikin safarar makaman da 'yan gwagwarmaya ke amfani dasu a yankin, wanda ya haɗa da Hizbullah dake Lebanon, kamar yanda haramtacciyar ƙasar ta Isra'ila tayi iƙirarin ta gano ta hannun jami'in ta da ya buga a jaridar Financial Times, ta bangaren jami'in da ya nemi a sakaya sunansa yace jaridar ta bankado inda yake baiwa mayakan Hezbollah miliyoyin daloli tun farkon fara yakin Gaza a watan Oktoba.


Ta dalilin haka ne yake fuskantar takunkumai daga kasar Amurka da Burtaniya na tsawon shekara, daga cikin abubuwan da aka sakawa takunkumai din har da harkokin kasuwancinsa.


Wata daya da ya wuce kamfanin Katerji holding group sun gabatar da wani aiki na wata babbar masana'anta a gabas ta tsakiya na farko a ire irensa a Syria cikin masana'antar  Sheikh Najjar Industrial City a cikin Aleppo wurinda ya kasance babban wurine yankin. Kamar yanda dan Jaridar Syria Muhammad Dabaa ya rubuta a ranar Talata.


Aikin ya kunshi kananan masana'antu 357, da suka samarda ayyukanyi fiyeda 300,000 kuma dukkan ayyukan kamfanonin ya damfaru ne kan amfani da wutar da suka samar mai karfin mega 150watt, atsawon watanni goma sha biyu.


Kisan na Alkaterji ya faru ne  sanadiyyar haramtattun farmakin da Isra'ila take kaiwa yankin Syria.



A hare haren na Isra'ila wani sojin kasar Syria ya samu shahada, yayinda wasu uku suka samu raunuka a harin bom da aka kai Damascus ranar 14 ga watan July da muke ciki, Sojin Isra'ila sun tarwartsa wurare da dama mallakin sojin Syria a yankin Golan da suka mamaye a ranar 10 ga watan na July.


Kafin nan, haramtacciyar Kasar Israila ta farmaki tashar jiragen ruwa a cikin garin Baniyas a gabashin Syria ranar 9 ga watan na July wanda ya haifarda hasarar kayayyakin amfani a gurin.

Post a Comment

0 Comments